Rikicin PDP: Jigo a Jam'iyyar Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ba a Hukunta Wike Ba
- Wani jigo a jam’iyyar PDP, Honorabul West Frimabo Paul, ya bayyana dalilin da ya sa jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa domin ci gaba da riƙe Nyesom Wike
- Jigon na PDP ya ce jam'iyyar na ganin daraja da mutuncin ministan na babban birnin tarayya Abuja domin shi babbar kadara ce a wajenta
- A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi, ya kuma ce tsohon gwamnan na jihar Rivers zai ci gaba da cin gajiyar duk wata alfarmar kasancewarsa ɗan PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban jam’iyyar PDP a mazaɓar Ajeromi ta ƙaramar hukumar Ifelodun a jihar Legas, Honorabul West Frimabo Paul, ya ce Nyesom Wike kadara ce ga jam’iyyar amma bai fi ƙarfin hukunci ba.
Jigon na PDP ya ce jam'iyyar tana mutunta tsohon gwamnan na jihar Rivers kuma za ta yi duk abin da za ta iya yi domin ganin ya ci gaba da zama a jam'iyyar.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa PDP ke son ci gaba da riƙe Wike?
Sai dai, jigon na PDP ya ce ci gaba da zaman Wike a jam'iyyar zai dogara ne a kan bincike da matakin da kwamitin ladabtarwa zai ɗauka.
"Wike bai fi ba kuma ba zai taɓa fin ƙarfin shugabannin jam'iyyar PDP ba. Wike mamba ne kuma za a ɗauke shi a matsayin mamba. Jam'iyyar na ganin mutuncinsa kuma za ta ci gaba da yin hakan."
"Jam'iyyar na ganin darajarsa kuma za ta ci gaba da mutunta shi. Tabbas Wike kadara ce amma bai fi ƙarfin hukunci ba. PDP na son Wike kuma za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ya ci gaba da zama mamba amma hakan ya dogara ne kan bincike da matakin da kwamitin ladabtarwa ya yanke."
- West Frimabo Paul
Meyasa PDP ba ta hukunta Wike ba?
West ya kuma bayyana cewa PDP ba ta hukunta Wike ba ne duk da ya ƙi bin umurninta saboda tana bin kundin tsarin mulki ne wajen gudanar da ayyukanta.
Ya yi bayanin cewa Wike zai ci gaba da cin gajiyar zama ɗan jam'iyyar har sai idan kwamitin ladabtarwa ya same shi da laifin cin dunduniyar jam'iyyar.
Batun rikicin siyasar Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya bayyana cewa rikicin siyasar da aka daɗe ana yi a jihar ya zo ƙarshe.
Gwamnan wanda yake takun saƙa da magabacinsa Nyesom Wike, ya yi nuni da cewa yanzu lokaci ne na yin aiki ga jama'a.
Asali: Legit.ng