Tinubu Yana Amfani da Wike Wajen Ruguza Jam’iyyar PDP? Dele Momodu Ya Magantu

Tinubu Yana Amfani da Wike Wajen Ruguza Jam’iyyar PDP? Dele Momodu Ya Magantu

  • Wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP ya yi kakkausar suka ga shugaban kasa Bola Tinubu kan faduwar Atiku Abubakar a zaben 2023
  • Haka zalika, ya zargi Tinubu da kulla wata makarkashiya a lokacin da ya shiga tsakanin Nyesom Wike da Siminilayi Fubara
  • A ranar Alhamis, Dele Momodu ya dage kan cewa matakin da Shugaba Tinubu ya dauka manuniya ce ta son wargaza jiga-jigan PDP

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya dora alhakin duk matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a kan yunkurin da jam'iyyar APC mai mulki ta yi na kawo cikas ga 'yan adawa a kasar.

Dele Momodu ya danganta Tinubu da rikicin PDP
Dele Momodu ya magantu yayin da alakar Tinubu da jigon PDP, Nyesom Wike ke kara karfi. Hoto:Dele Momodu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Momodu, ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a a shirin 'siyasa a yau' na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Jiga jigan APC 5 da ake zaton za su raba gari da Tinubu a zaben 2027

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya zargi jam’iyya mai mulki karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin murkushe ‘yan adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“APC za ta yi duk mai yiwuwa don ruguza 'yan adawa; su sayi wadanda za su iya saya, su tsoratar da wadanda ba za su iya saya ba tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta wargaje."

- Dele Momodu.

Mecece alakar Wike-Tinubu a rikicin PDP?

Legit Hausa ta fahimci cewa, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kasa shawo kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar tun bayan faduwa zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Nyesom Wike, ministan Abuja ya kara dagula lamuran jam'iyyar yayin da ya karbi mukami a gwamnatin Tinubu bayan da aka yi zargin ya yaudari a zaben na 2023.

Momodu: "Tinubu na kokarin ruguza PDP"

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya fice daga jam'iyyar PDP

Da yake karin haske a ranar Alhamis, Momodu ya zargi Tinubu da murkushe ‘yan adawa duk da cewa shi ma dan adawa ne kafin jam’iyyarsa ta kawar da PDP daga mulki.

Momodu ya kara da cewa Gwamna Similanayi Fubara da wanda ya gada, Nyesom Wike na fada ne kan yadda ake tafiyar da baitul malin jihar, inji rahoton Daily Trust.

"Tinubu na amfani da Wike a Ribas. Suna son ya samu iko da jihar ba wai kawai domin nema masu kuri’u ba, har ma da ba su damar shiga baitul malin jihar Ribas.”

- Dele Momodu.

Borno na biyan 'yan fansho N4000

A wani labarin kuma, kungiyar kwadago a jihar Borno ta koka kan yadda har yanzu gwamnatin jihar ke biyan wasu 'yan fansho N4000 kacal a wata.

Kungiyar ta roki Gwamna Babagana Umara Zulum da ya duba batun kudaden da ake biyan tsofaffin ma'aikatan jihar tare da daukar matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.