Tinubu vs El Rufai: Jigon APC Ya Yi Hasashen Yadda 'Yan Najeriya Za Su Yi Zaben 2027

Tinubu vs El Rufai: Jigon APC Ya Yi Hasashen Yadda 'Yan Najeriya Za Su Yi Zaben 2027

  • Ana ci gaba da tattauna batun yiwuwar Nasir Ahmad El-Rufa'i ya nemi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa
  • Hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin sauya shekar tsohon gwamnan na jihar Kaduna zuwa jam’iyyar SDP
  • Jigon jam’iyyar APC, Podar Yiljwan Johnson, a wata hira da Legit.ng, ya bayyana yadda ƴan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Podar Yiljwan Johnson, jigo a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Plateau, ya yi magana kan batun yin takarar Nasir Ahmad El-Rufai a zaɓen 2027.

Podar ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, yana da ƴancin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP ya fadi jihar da jam'iyyar za ta kwace a hannun APC

Jigon APC ya yi magana kan zaben 2027
Ana rade-raden El-Rufai zai yi takara da Tinubu a zaben 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

An fara raɗe-raɗin takarar El-Rufai

Ku tuna cewa El-Rufai ya dawo fagen siyasar Najeriya kwanan nan bayan ya je hutu ya dawo, sakamakon rashin samun kujerar minista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan na Kaduna na shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, bayan ya goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

Biyo bayan rashin jituwar da El-Rufai ya yi da Tinubu, tsohon gwamnan ya shiga cikin jerin manyan ƴan siyasa da za su iya yin adawa da sake zaɓen Tinubu a 2027.

Sai dai, tsohon gwamnan bai bayyana aniyarsa ta yin takara ba, har ma ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake na cewa zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar SDP kafin 2027.

Ya ƴan Najeriya za su yi zaɓe a 2027?

Da yake magana da Legit.ng a wata tattaunawa ta musamman kan lamarin, a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu, Podar Johnson ya ce:

Kara karanta wannan

Jigon APC ya kawo muhimman dalilai 2 da za su sanya a sake zaben Tinubu a 2027

"Dangane da El-Rufa’i, shi ɗan Najeriya ne, mai ƴancin bayyana ra'ayinsa na tsayawa takara. Yanzu ya rage ga ƴan Najeriya su yi la’akari da halayensa na baya da na yanzu domin yanke hukunci."
"Na tabbata a shekarar 2027, ƴan Najeriya ba za su yi zaɓe bisa addini ba, sai dai a kan halaye da manufofi domin samun kyakkyawar makoma."

- Podar Yiljwan Johnson

Za a sake zaɓen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon na jam'iyyar APC, Podar Yiljwan Johnson ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin mulkin Tinubu musamman yadda ya farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng