Jigon APC Ya Kawo Muhimman Dalilai 2 da Za Su Sanya a Sake Zaben Tinubu a 2027
- Wani jigo a jam’iyyar APC ya ce ƴan Najeriya sun gamsu da gwamnati mai ci a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu duk da hauhawar farashin kayayyaki da ya yi ƙamari a ƙasar nan
- Masana harkokin siyasa dai sun yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu irin rawar da shugaban ya taka za ta sanya ya samu gagarumar nasara a babban zaɓe mai zuwa
- Da yake tattaunawa da Legit.ng a ranar Litinin, 29 ga Afrilu, jigo a jam’iyyar APC, Podar Yiljwan Johnson, ya bayyana dalilai biyu da za su sanya ƴan Najeriya su zaɓi Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jos, jihar Plateau - Jigo a jam'iyyar APC, Podar Yiljwan Johnson, ya ce ƴan Najeriya za su sake zaɓen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2024, Shugaba Bola Tinubu zai cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya.
Batun sake zaɓen Tinubu ya jawo cece-kuce
Sai dai, kawo yanzu sauye-sauyen da Tinubu ya yi a kan tattalin arziƙin ƙasar nan ya haifar da ƙaruwar farashin man fetur da da faɗuwar darajar Naira a kan Dala, lamarin da ya jawowa jama’a ƙuncin rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka ne ƙungiyar Dattawan Arewa ta ce sun yi nadamar zaɓen Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda suka yi barazanar juya masa baya a zaɓen 2027.
2027: Shin za a sake zaɓen Tinubu?
A wata hira ta musamman da Legit.ng tayi da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2024, tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Filato, Podar Yiljwan, ya kawo dalilan da ya sa za a sake zaɓen Tinubu.
Podar Yiljwan ya ce duk da cewa ƙasar nan ta faɗa cikin mawuyacin hali a ƴan kwanakin nan saboda taɓarɓarewar tattalin arziƙi, za a sake zaɓen Tinubu saboda ƴan Najeriya sun yarda da manufofinsa.
Ya kawo dalilan farfaɗowar tattalin arziƙi da manufofin Tinubu kan tattalin arziƙin ƙasar nan, a matsayin abin da zai sanya ƴan Najeriya su sake yi masa ruwan ƙuri'u a 2027.
"Tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa, amma idan za a faɗi gaskiya abin da kawai ake buƙata shi ne ƴan Najeriya su ƙara haƙuri. Nan ba da jimawa ba za mu ga sakamakon."
"Wasu daga cikin manufofin gwamnatin nan na kwanan nan za su ƙara haɓɓaka tattalin arziƙi."
"Bisa ga la'akari da manufofinsa kan tattalin arziƙi, ina da tabbacin cewa ƴan Najeriya za su yarda da shi su sake zaɓensa a 2027. Addu'a ta a gare shi ita ce Allah ya shiga lamarinsa, mafi muhimmanci ya ba shi tsawon rai."
- Podar Yiljwan Johnson
Jigon PDP ya dira kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jami'yyar PDP, Segun Showunmi ya magantu kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya yaudari na hannun damansa.
Showunmi ya nuna takaici musamman kan yadda shugaban ya ci amanar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello duk da wahalar da suka sha a dalilin shi.
Asali: Legit.ng