Mu Bar Barci: Tsohon Gwamna Ya Yi Kira Ga Shugabannin Arewa Su Farka
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya yi kira na musamman ga shugabannin Arewa kan cigaban yankin
- Tsohon gwamnan ya yi kiran ne yayin da yake ganawa da 'yan jarida a jihar Sokoto a wata tattaunawa da ta shafi Arewa
- Ya kuma kara da yin kira na daban ga gwamnatin tarayya a kan lamarin tsaro da samar da abinci a fadin Najeriya baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya yi kira ga shugabannin Arewa wurin magance matsalolin yankin.
Attahiru Bafarawa ya kara da cewa ya kamata yankin Arewa ya kasance yana kafada-da-kafada da sauran yankunan Najeriya.
Game da rashin tsaro kuma ya ce ya zama wajibi ga gwamnonin jihohi da gwamnatin tarayya su yi haɗaka wurin dakile matsalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa tsohon gwamnan ya yi kiran ne yayin da yake ganawa da 'yan jarida a Sokoto.
Bafarawa ya ce a nisanci siyasar kudi
'Dan siyasar ya kuma koka kan yadda yan siyasa a yanzu suka mayar da shugabanci harkar neman kudi maimakon gina kasa.
A cewarsa, lokacin da suka fara siyasa sun shiga harkar ne domin gina kasa ba neman hanyar tara dukiya ba.
Bafarawa ya ce abin mamaki ne yadda 'yan siyasa ke kashen makudan kudade wurin neman kujerar shugabanci.
Ya yi kira ga yan siyasa a kan su sani lalle akwai ranar hisabi kuma za su girbi abin da suka shuka.
Saboda haka ya ce ya kamata kowa ya koma mazabarsa ya bincika alkawarin da ya yi kuma ya yi kokarin cikawa.
Alakar tsaro da noma a yankin Arewa
Tsohon 'dan takaran shugaban kasar ya kara da cewa matsalar tsaro ta na barazana ga harkar samar da abinci kuma dole sai gwamnati ta tashi tsaye domin magance ta, cewar jaridar Tribune
A cewarsa, matsalar tsaro a yankin Kaduna ta sa ba zai iya zuwa gonarsa ba kuma akwai manoma da dama irinsa wanda abin ya shafa.
Matsalar ruwa ta yi wa Arewa katutu
A wani rahoton, kun ji cewa matsalar ruwa ta kara ta'azzara a jihar Sokoto har ya fara kaiwa ga daina ayyuka a wasu masana'antu.
Hakan kuma ya biyo bayan yanke ruwan da hukumar samar da ruwa ta jihar ta yi ne ga wasu kamfanoni.
Asali: Legit.ng