Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Shugabannin Kananan Hukumomi 11 a Gombe

Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Shugabannin Kananan Hukumomi 11 a Gombe

  • Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi
  • Rantsuwar ta biyo bayan nasara ce da 'yan takarar suka samu a zaben da ya gabata a jihar ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu
  • Legit ta tattauna da Bilyaminu Yahaya, wani dan jam'iyyar PDP, domin jin yadda sakamakon zaben ya kasance a garesu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi a jihar Gombe.

Gombe LG polls
Shugabannin kananan hukumomi sun yi ranstuwa a jihar Gombe Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Asali: Facebook

Shugabannin su 11 sun yi rantsuwar fara aiki ne bayan nasara da suka samu a zaben kananan hukumomi da ya gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi alkawari na 2 a jere a kan matsalar ruwa a jihar Gombe

Gombe: Jami'yyar APC ce ta lashe zabe

Mai taimakawa gwamnan a harkar sadarwa, Isma'ila Uba Misilli, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa an gabatar da zaben ne na shugabannin kananan hukumomi da kasiloli a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon zaben ya nuna dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC mai mulkin jihar ne suka yi nasara.

Kiran gwamna Inuwa ga sabbin shugabannin

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kira ga sabbin shugabannin da su rike gaskiya da amana da kuma yi kokarin sauke nauyin dake kansu.

Ya kuma kara da cewa nasarar da suka samu ta nuna cewa al'ummar jihar sun aminta da su saboda haka su dauke ta a matsayin nauyin amana da ya rataya a wuyansu.

Har ila yau Inuwa ya yi kira garesu da su yi amfani da damar wurin hada kan al'umma ba tare da nuna bambanci ba.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwamiti ya dauki mataki kan zargin badakala, ya fadi tsare tsaren Bincike

Taron rantsuwar ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, masu sarauta da manyan 'yan siyasa a fadin jihar.

PDP ta yi watsi da sakamakon zaben

A hirar da Legit ta yi da wani dan jam'iyyar PDP, Bilyaminu Yahaya, ya ce su basu gamsu da zaben ba balle ma su yarda da sakamakonsa.

A cewar Bilyaminu, a mazabu da yawa cikin karamar hukumar Gombe ko akwati ba a kawo ba balle ma a kada kuri'a.

Ya kuma kara da cewa abin da jam'iyyar APC mai mulki ta yi alama ce da ke nuna ta ji tsoron gudanar da zaben gaskiya domin jama'a sun dawo daga rakiyarta.

An bude titin Gauduje a jihar Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bude titin da aka radawa sunansa a jihar Gombe.

Gwamnan jihar ya ce Ganduje ya zo jihar ne domin karfafa 'yan takarar APC a zaben kananan hukumomi da za a gudanar a jihar.

Ganduje ya mika godiya ga daukacin al'ummar jihar tare da kiransu a kan su cigaba da goyon bayan gwamnan da shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng