Ondo: Jam'iyyar APC Za Ta Bayar da Satifiket Din Lashe Zaben Fidda Gwani
- Jam'iyyar APC mai mulki za ta gabatar da satifiket ɗin lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Ondo, ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa
- Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na ƙasa ne ya tabbatar da cewa za a ba gwamnan satifiket ɗin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Afirilun 2024
- Gwamnan shi ne dai ya zama ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a zaɓen da za a gudanar a watan Nuwamban 2024
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Jam’iyyar APC za ta miƙawa wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa, satifiket ɗin lashe zaɓe a ranar Litinin.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasarar lashe zaɓen ne wanda aka gudanar domin fidda ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba.
Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na ƙasa, Nze Duru ne ya bayyana hakan ga jaridar The Punch a ranar Lahadi, 28 ga watan Afirilun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe APC za ta bada satifiket?
"Eh ranar Litinin ne za a gabatar da takardar shaidar cin zaɓen ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja."
- Nze Duru
Sai dai Duru bai bayyana ko za a gabatar da satifiket ɗin ne a gabanin taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ko a lokacin taron ko bayan an kammala, wanda shi ma za a yi a ranar Litinin.
Hakan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ƴan takarar da suka fafata a zaɓen da su marawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa baya.
Ondo: Lucky ya yi sa'ar tikitin APC
Kwamitin zaɓen fidda gwanin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo ne ya ayyana Ayiedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan kammala gudanar da zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 18.
Sai dai, wasu daga cikin ƴan takarar sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen bisa zargin tafka maguɗi da tashe-tashen hankula a wasu rumfunan zaɓe.
APC za tayi rashin nasara a Ondo?
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Ondo, ya hango rashin nasara ga jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar.
Bamidele Oloyeloogun ya yi nuni da da cewa APC ka iya yin rashin nasarar ne idan ba a soke zaɓen fidda gwani na gwamna da ta yi ba a jihar.
Asali: Legit.ng