Ganduje: Mummunar Zanga zanga Ta Barke a Sakatariyar APC Kan Shugaban Jam'iyya
- Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake cin karo da wata matsala a yau Alhamis 25 ga watan Afrilun 2024
- Daruruwan matasa sun cika sakatariyar APC da ke Abuja inda suka bukaci Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan tsagin jam'iyyar a Kano ya sake dakatar da tsohon gwamnan kan wasu sabbin zarge-zarge
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Daruruwan matasa ne suka mamaye sakatariyar jam'iyar APC da ke Abuja domin yin zanga-zanga.
Matasan sun cika bakin sakatariyar jam'iyar ne inda suka bukaci shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
APC: Wace bukata suka nema daga Ganduje?
Mutanen sun bukaci hakan ne bayan wani tsagin jami'yyar APC a gundumar Ganduje a Kano ya dakatar da tsohon gwamnan jihar, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar suna daga kwallaye tare da neman Ganduje ya yi murabus domin dawo da shugabancin jam'iyyar Arewa ta Tsakiya, cewar Vanguard.
Sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume su tabbatar da dawo da shugabancin jam'iyyar zuwa yankin.
...Sun ce zaman Ganduje saba ka'ida ne
Yayin da suke tattaunawa da manema labarai, masu zanga-zangar karkashin kungiyar Concerned North Central APC sun ce zaman Ganduje kan shugabancin jam'iyyar saba ka'ida ne, cewar Daily Post.
Kungiyar ta bayyana cewa kasancewarsa shugaban jam'iyyar har yanzu ya sabawa ka'idar APC wurin mayar da shugabancinta yankin.
Shugaban masu zanga-zangar, Mohammed Mahmud Saba ya ce su a yankin Arewa ta Tsakiya ba su tare da Ganduje.
Wannan na zuwa ne yayin da shugabannin jam'iyyar APC a jihohin Najeriya suka nuna goyon bayansu ga shugaban na kasa.
An bukaci sasanta Ganduje da Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa jigon jami'yyar APC, Salihu Lukman ya yi magana kan takarar shugabancin Sanata Rabiu Kwankwaso.
Lukman ya ce zai yi wahala Kwankwaso ya yi tasiri a jam'iyyar NNPP kan muradinsa na neman shugabancin Najeriya.
Ya ce jam'iyyar APC za ta iya taimaka masa wurin bude masa kofa domin ya shigo tare da gyara matsalolinsa a ƙasar.
Asali: Legit.ng