Wike vs Fubara: Kwamishinoni 4 Sun Tattara Sun Ajiye Aiki a Gwamnatin Jihar Ribas

Wike vs Fubara: Kwamishinoni 4 Sun Tattara Sun Ajiye Aiki a Gwamnatin Jihar Ribas

  • Kwamishinoni guda hudu sun ajiye aiki da gwmantin jihar Ribas karkashin jagorancin gwamna Siminalayi Fubara
  • Ana kallon ajiye aikin na da nasaba da rikicin da yake faruwa tsakanin gwamnan jihar da ministan Abuja Nyesom Wike
  • Gwmantin jihar ta yi martani cikin gaggawa a kan lamarin ta hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Joseph Johnson

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kwamishinoni hudu a majalisar zartarwar jihar Ribas sun ajiye aikin da gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya nada su.

Fubara and Wike
Gwamnatin jihar Ribas ta ce kwamishinonin su na da 'yancin ajiye aiki ko karba. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wanda suka ajiye aikin sun hada da kwamishinan ayyuka George Kelly, kwamishinan wutar lantarki Henry Ogiri, kwamishinan shari'a Farfesa Zacchaeus Adango da kwamishinan kudi Isaac Kamalu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Dalilin ajiye aikin Kwamishinonin Fubara

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mista Kelly da Ogiri sun ajiye aikin ne saboda sabon mukami da suka samu a gwamnatin tarayya alhali mista Kamalu da Farfesa Adango sun ajiye aikin ne saboda canja musu ma'aikata da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan jihar ya sauya wa kwamishinan Shari'a ma'aikata zuwa ofishin ayyuka na musamman kafin daga bisani ya ajiye aikin.

Farfesa Adango dai dama ya taba ajiye aikin a lokacin da rikici ya yi ƙamari tsakanin gwamnatin jihar da ministan Abuja, Nyesom Wike kafin daga baya shugaba Tinubu ya sa baki a lamarin.

Amma sai dai ana zargin a lokacin da Farfesa Adango ya dawo aiki sai ya cigaba da biyayya ga ministan Abuja maimakon gwamnan jihar.

A wannan karon dai Adango ya ajiye aikin ne bisa dalilin cewa an canja masa ma'aikata ba tare da sanar da shi ko neman yardarsa ba, cewar jaridar Premium times

Kara karanta wannan

Dan a mutun tsohon gwamna ya yi murabus, ya ajiye kujerarsa a gwamnatin PDP

Martanin gwamnatin Fubara a Ribas

Amma dai gwmanatin jihar ta Ribas ta ce ajiye aikin nasu ba zai yi tasiri a harkar gudanar da gwamnatin ba kuma ba zai hana ayyukan cigaba a jihar ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Joseph Johnson, ya yi martani yana mai cewa ba dole bane ga duk wanda aka ba wa mukami sai ya karba, suna da 'yancin kin karba kamar yadda gwamnatin ta ke da 'yancin nada su.

Fubara ya magantu kan tsige shi a Ribas

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi magana a kan rikicin siyasar da ya dabaibaye shi da magabacinsa, Nyesom Wike

Fubara ya kuma ce a shirye yake ya bar muƙaminsa na gwamna domin samun zaman lafiya a jihar ta yankin Kudu maso Kudu na Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng