Shugabannin APC Na Jihohi 36 Sun Faɗi Matsayarsu Kan Dakatar da Ganduje
- Shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun kaɗa kuri'ar amincewa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙaaa
- Sun tabbatar da wannan matsaya ne yayin da suka ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Talata
- A cewarsu, ba za su zuba ido suna kallo a ci mutuncin shugaban na APC kamar yadda aka yi wasu shugabannin APC da suka gabata ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyar shugabannin All Progressives Congress (APC) na jihohi ta kada kuri’ar amincewa da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje.
Tawagar wakilan shugabannnin APC na jihohi 36 da Abuja ne suka tabbatar da goyon bayansu ga Ganduje yayin da suka kai masa ziyara hedkwatar APC da ke Abuja ranar Talata.
"Muna tare da Ganduje" - Shugabannin APC
Jam'iyyar APC ta bayyana haka a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, muƙaddashin shugaban ƙungiyar kuma shugaban APC na jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya ce suna tare da shugabancin Ganduje kuma za su kare shi duk rintsi.
Jawabin shugaban APC a kan Ganduje
"Mun zo nan ne domin mu kara tabbatar maka da cewa har yanzun kai ne kyaftin na jirgin. Bayan haka ma waɗanda suka sanar (an dakatar da Ganduje) ba a sansu ba a APC.
"Ba za mu bari a ci mutuncin ka ba kamar yadda aka yi wa wasu shugabannin jam'iyyar da suka gabata. Abin da suka ƙulla shi ne su yi maka juyin mulki amma suka ji kunya.
"Mun zo nan ne mu kara tabbatar da mubaya'ar mu gare ka cewa muna tare da kai a kowane lokaci duk rintsi duk wuya."
- Cornelius Ojelabi
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan babbar kotun jihar Kano ta yi amai ta lashe, ta tabbatar da tsohon gwamnan a matsayin shugaban APC na ƙasa.
Ɗan takarar APC a Ondo ya bayyana
A wani rahoton kuma Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya zama ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamna da za a gudanar a watan Nuwamban 2024.
Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen fidda gwani na APC bayan ya samu ƙuri'u 48,569 inda ya doke sauran abokan takararsa har mutum 15.
Asali: Legit.ng