Zaɓen Bayelsa: Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan PDP
- Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Bayelsa ta shirya yanke hukunci a ƙarar da ɗan takarar APC, Timipre Sylva, ya shigar
- Mai shari'a Adekunle Adeleye ya bayyana cewa cikin kwanaki 180 kotu za ta sa rana kuma ta yanke hukunci kamar yadda doka ta tanada
- Gwamna Diri na jam'iyyar PDP ya samu nasarar tazarce a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da aka yi a watan Nuwamba, 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Bayelsa ta tanadi hukunci a ƙarar da ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Timipre Sylva, ya shigar.
Sylva, tsohon ƙaramin ministan man fetur ya kalubalanci nasarar Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a zaben da aka yi a watan Nuwamba, 2023.
Alƙalin kotun zaɓen mai shari'a Adekunle Adeleye ya sanar da cewa za a yanke hukuncin kowane lokaci daga nan zuwa kwanaki 180 kamar yadda doka ta tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa za a sanar da kowane ɓangare da zarar kotun ta zaɓi ranar da za ta karanto hukunci a shari'ar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Yadda zaman karshe ya gudana a kotu
A zaman da kotun ta yi ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, 2024 kowane ɓangare ya miƙa rubutaccen bayanansa na ƙarshe ga alkali.
Yayin da jam'iyyar APC da ɗan takararta suka roƙi kotun ta amince da buƙatarsu saboda zaɓen cike yake da kura-kurai, PDP da Gwamna Diri sun nemi a kori ƙarar domin APC ba ta hujjoji.
Gwamna Diri ya hau mulkin Bayelsa a 2020 a karon farko, sannan kuma ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan da aka yi a watan Nuwamban 2020 ya zarce zango na biyu.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Diri na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 175,196 yayin da Sylva, ɗan takarar APC ya samu ƙuri'u 110,108.
Amma bayan hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakamako, tsohon ministan ya kalubalanci ayyana Diri a matsayin wanda ya lashe zaɓen a gaban kotu.
Ana neman sauke Ganduje a APC
A wani rahoton kuma masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano.
Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu.
Asali: Legit.ng