Osun: Ruɗani Yayin da 'First Lady' 2 Suka Bayyana Wajen Tarbar Remi Tinubu, an Samu Mafita
- An shiga rudani bayan samun 'First Lady' guda biyu a jihar Osun yayin tarbar matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu
- An gano wasu takardu da ke yawo inda suke tarbar Remi zuwa jihar daga ofisoshin dukkan matan gwamnan guda biyu
- Daga bisani gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa inda ta fayyace asalin 'First Lady' a jihar wacce za ta tarbi Remi Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - An ga hatsaniya a jihar Osun yayin da matan Gwamna Ademola Adeleke suke shirye-shiryen tarbar matar shugaban kasa, Remi Tinubu.
Matan guda biyu dukkansu sun buga takardun tarbar matar shugaban kasa, Bola Tinubu.
Musabbabin samun rudani a Osun
Hakan ya biyo bayan kokarin tarbar Remi Tinubu da matan biyu Titilola Adeleke da Ngozi Adeleke suka yi, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran matar shugaban kasar za ta ziyarci birnin Osogbo na jihar a yau Talata 23 ga watan Afrilu.
Sai dai Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa Titilola ce za ta tarbi Remi Tinubu a matsayinta na uwargidar jihar.
Martanin Gwamnan Osun kan lamarin
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar a jiya Litinin 22 ga watan Afrilu.
Rasheed ya ce babu wani cece-kuce kan matsayar ofishin uwargidar gwamna a jihar kamar yadda ake yadawa, a cewar Daily Trust.
Ya ce Titilola ita ce uwargida kuma ita ce za ta karbi bakwancin matar shugaban kasa a yau Talata 23 ga watan Afrilu.
Olawale ya ce sanarwar da aka fitar a baya ba daga ofishin Ngozi Adeleke ya fito ba, inda ya ce an cafke wanda ya haɗa rigimar kuma ya na shan tambayoyi.
APC ta kalubanci Gwamna Adeleke kan addininsa
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Osun ta kalubalanci Gwamna Ademola Adeleke kan ainihin addinin da ya ke bi guda daya.
Jam'iyyar ta bayyana haka ne yayin da gwamnan ke ayyana kansa a matsayin Musulmi kuma Kirista a lokaci guda.
A martaninta, jam'iyyar PDP ta ce APC ba ta da manufa shiyasa ta fake da maganar addini domin kawo rudani a jihar Osun.
Asali: Legit.ng