Fusatattun 'Yan APC Sun Lakadawa Kwamishina Dukan Tsiya, An Fadi Laifinsa

Fusatattun 'Yan APC Sun Lakadawa Kwamishina Dukan Tsiya, An Fadi Laifinsa

  • A ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, ƴan jam’iyyar APC a mazaɓar Ugbo ta uku a ƙaramar hukumar Ilaje, sun yi wa kwamishinan lafiya na jihar Ondo, Banji Ajaka, dukan tsiya
  • An ce ƴan jam’iyyar sun kai wa Ajaka hari ne a lokacin da jami’in INEC ya bayyana cewa yana riƙe da takardar sakamakon zaɓen
  • Kwamishinan wanda ya bayyana hakan ya ce ba a ba shi damar bayyana abin da ya faru ba kafin maharan su far masa da duka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Ugbor ta uku a ƙaramar hukumar Ilaje a jihar Ondo ya rikiɗe zuwa tarzoma a ranar Asabar 20 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindinga sun kashe 'yan banga 3 tare da sace mutane masu yawa a wani sabon hari

Hakan ya faru ne yayin da wasu fusatattun ƴaƴan jam’iyyar APC suka yi wa kwamishinan lafiya na jihar, Banji Ajaka, duka a mazaɓar bisa zargin ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

An yi wa kwamishina duka a Ondo
'Yan takara 15 suka fafata a zaben fidda gwanin APC na gwamnan Ondo Hoto: Olusola Oke 4 Governor, Ondo State, Jimoh Ibrahim CFR, OFR, Hon Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

An tattaro cewa a lokacin da jami’an zaɓe suka zargi Ajaka da riƙe takardar sakamakon zaɓen fidda gwanin, sai fusatattun ƴaƴan jam’iyyar APC a mazaɓar waɗanda suka buƙaci ya ba su ita suka kai masa hari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan APC suka doki kwamishinan?

Da yake magana kan lamarin, wani ganau ya shaida wa jaridar The Cable cewa ƴan jam’iyyar ne suka kai wa kwamishinan hari a lokacin da wani jami’in hukumar INEC ya ambaci sunansa.

Shaidan ya bayyana cewa:

"Honarabul Ajaka, kwamishinan lafiya, ya sha dukan tsiya a garinsa yayin da jami’in INEC ya ambato sunansa."
"Wasu jami'an INEC da ƴan tawagar Aiyedatiwa sun haɗa baki inda suka cire takardar sakamakon zaɓen daga cikin kayayyakin da aka ba su."

Kara karanta wannan

Benue: Tashin hankali yayin da ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriyar APC

"Wajen cike yake da magoya bayan Cif Olusola Oke. Mutanen wajen sun fusata saboda sun yi amanna cewa lokaci ya yi da Oke zai mulki jihar nan."

Ajaka ya magantu kan lamarin

A nasa ɓangaren, Ajaka ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bayyana lamarin a matsayin rashin mutunci wanda bai kamata ba, inda ya ƙara da cewa ba a ba shi dama ya kare kansa ba.

Jaridar Punch ta ambato kwamishinan yana cewa:

"Eh, an kai min hari ne saboda sun yi zargin cewa ina riƙe da takardar sakamako."
"Mutane sun yi min duka. Sun zarge ni da riƙe sakamakon zaɓe, kuma a lokacin da na ke ƙoƙarin bayyana musu abin da ya faru, sai kawai suka fara lakaɗa min duka."

- Banji Ajaka

Hasashe kan zaɓen Ondo da Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban cocin Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen abin da zai faru a zaben jihohin Edo da Ondo.

Ayodele ya ce akwai alamun cewa Gwamna mai ci a jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa shi ya ke da nasara a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng