Shugaban PDP Ya Zargi APC da Kokarin Kawo Rabuwar Kawuna a Jam'iyyar Adawa
- Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya nuna yatsa ga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Ambasada Umar Damagum ya zargi APC da ƙoƙarin kawo ruɗani a jam'iyyar ta hanyar rarraba kawunan mambobinta
- Ya buƙaci mambobin jam'iyyar da su haɗa kansu domin samar da adawa mai kyau saboda ƴan Najeriya na son PDP har yanzu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ambassada Umar Iliya Damagum, ya yi zargin cewa jam'iyyar APC na son rarraba kawuna a jam'iyyar adawan.
Iliya Damagum ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar PDP a birnin tarayya Abuja.
Muƙaddashin shugaban na PDP ya kuma zargi gwamnatin APC da jefa ƙasar nan cikin halin wuya, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Damagum ya ce wajen taron PDP?
Damagum ya gayawa mambobin jam'iyyar cewa ya kamata su fahimci cewa ƴan Najeriya na jiran su zo su ceto ƙasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki.
Ya yi kira da a kafa kwamiti mai ƙarfi wanda zai sulhunta ƴaƴan jam'iyyar waɗanda ba sa ga maciji da juna.
"Akwai buƙatar a kafa kwamitin sulhu mai ƙarfi wanda zai haɗa kan fusatattun mambobinmu, musamman waɗanda suka samu saɓani a lokacin zaɓen fidda gwani da ya gabata. Har yanzu ba a makara ba."
"Dole ne mu sake fasali da ƙarfafa jam'iyyar domin yin adawa mai ma'ana wacce za ta kawo sababbin tsare-tsare wajen gudanar da mulkin ƙasar nan."
"Dole ne mu fahimci cewa ƴan Najeriya na son PDP kuma suna jiran da mu kawo musu ɗauki kan wahalhalun da APC ta jefa su a ciki."
- Ambassada Umar Iliya Damagum
Jaridar Daily Post ta ce a wajen taron na NEC, shugaban kwamitin amintattu na PDP, Adolphus Wabara, ya bayyana cewa ƴan Najeriya na jiran PDP ta kawo musu ɗauki kan halin da gwamnatin APC ta jefa su.
Batun kujerar shugaban PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa babu wani shiri na sauya shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa a wurin taron majalisar zartaswa (NEC) da za a gudanar.
Gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ne suka tabbatar da haka.
Asali: Legit.ng