Dino Melaye Ya Caccaki Tsohon Gwamnan PDP da Wike da Atiku Suka Hadu, Bidiyon Ya Yadu

Dino Melaye Ya Caccaki Tsohon Gwamnan PDP da Wike da Atiku Suka Hadu, Bidiyon Ya Yadu

  • A wani taron PDP, Sanata Dino Melaye, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, kan cin dunduniyar da ya yi wa jam'iyyar a zaɓen 2023
  • A ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun halarci taron manyan ƙusoshin jam’iyyar PDP na ƙasa a Abuja gabanin taron NEC na jam’iyyar
  • A ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, 2024 ne aka shirya gudanar da babban taron NEC na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dino Melaye, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan Kogi a 2023, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Dino Melaye ya caccaki Ortom ne a lokacin da manyan masu ruwa da tsaki na shiyyar Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar adawan suka yi wani muhimmin taro a ranar Laraba 17 ga watan Afrilu a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun ɗauki matsayi kan batun sauya shugaban PDP na ƙasa a taron NEC

Melaye ya caccaki Ortom
Dino Melaye ya caccaki Samuel Ortom a wajen taron PDP Hoto: Dino Melaye, Flo 94.9 FM Umuahia
Asali: Facebook

Meyasa Dino Melaye ya caccaki Ortom?

A wajen taron, Dino Melaye ya ce ya yi mamakin yadda Ortom ya zauna cikin taron PDP ba tare da wani shakku ba duk da zargin cin dunduniyar jam'iyyar da ake masa a lokacin babban zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Sanatan ya ce ya kamata jam'iyyar PDP ta ɗauki matakin ladabtarwa kan Ortom.

Kalaman da Dino Melaye ya yi a fili ya sanya cacar baki ta ɓarke a tsakaninsu, inda suka yi musayar kalamai.

Hakazalika shugabannin jam’iyyar na shiyyar Arewa ta Tsakiya bayan tashi daga taron, sun dage cewa dole ne shiyyar ta samar da shugaban jam’iyyar na ƙasa a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC).

Kalli bidiyon a nan:

Atiku, Wike sun haɗu a taron PDP

Haka kuma a Abuja, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023, Atiku Abubakar da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun haɗu.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

Manyan ƴan siyasan biyu sun haɗu ne a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, bayan sun halarci taron manyan ƙusoshin jam’iyyar PDP na ƙasa a Abuja gabanin taron NEC na jam’iyyar.

Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan na jihar Ribas ya halarci taron jam'iyyar PDP tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Wike dai ya samu saɓani da shugabannin jam’iyyar PDP kuma bai goyi bayan Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ba a zaɓen 2023.

Batun shugabancin jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma kun ji cewa babu wani shiri na sauya shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa a wurin taron kwamitin zartaswa ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu.

Gwamnonin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ne suka tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng