Kebbi: Majalisa Ta Ɗauki Mummunan Mataki Kan Mambanta, Ta Lissafo Dalilai

Kebbi: Majalisa Ta Ɗauki Mummunan Mataki Kan Mambanta, Ta Lissafo Dalilai

  • Ɗan Majalisar jihar Kebbi, Hassan Umar ya gamu da fushin Majalisar bayan sun dakatar da shi a yau Litinin 15 ga watan Afrilu
  • Majalisar ta dauki matakin ne kan zargin Umar da neman hada husuma tsakanin mambobin Majalisar da shugabanninta
  • Magatakardar Majalisar, Shamaki Sulaiman shi ya tabbatar da haka a yau Litinin 15 ga watan Afrilu ga 'yan jaridu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dauki mataki kan wani mambanta mai suna Hassan Umar.

Umar wanda ke wakiltar Birnin Kebbi ta Arewa an dakatar da shi ne kan wasu kalamai da ya yi da ba su dace ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 da Tinubu ya kamata ya yi domin tabbatar da tsaron makarantu a Najeriya, kungiya

Majalisa ta dauki mataki kan wani mambanta a Kebbi
Majalisar jihar Kebbi ta dakatar da mambanta kan neman ta da husuma. Hoto: Kebbi State House of Assembly, Hassan Umar.
Asali: Facebook

Yaushe aka dakatar da mamban a Kebbi?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan Majalisar, Sulaiman Shamaki ya fitar a yau Litinin 15 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Post ta tattaro cewa an dauki matakin ne kan kalaman mamban da ke neman hada rikici tsakanin mambobi da shugabannin Majalisar.

"Ni Shamaki Sulaiman, magatakardan Majalisa, an umarce ni da na sanar da ku cewa an dakatar da Hassan Umar daga Majalisar."
"An dauki matakin ne a zaman da aka yi a ranar 12 ga watan Afrilu kan kalaman dan majalisar da ke wakiltar Birnin Kebbi ta Arewa."

- Shamaki Sulaiman

Wasu laifuffuka ya aikata a Majalisar?

Sanarwar ta lissafo laifuffukan dan majalisar da suka haɗa da ingiza mambobin Majalisar ga shugabanninta.

Har ila yau, hakan ya na neman kawo matsala tsakanin majalisar da kuma ta zartarwa, cewar rahoton Independent.

Kara karanta wannan

Bayan rikici kan nadinsa, Basarake ya rasu watanni kadan da karbar sarauta

Kalaman da ɗan Majalisar ya yi tasiri wurin neman kawo tsaiko a Majalisar musamman tsakanin mambobin da shugabanninsu.

Gwamna Idris ya gargadi malamai kan siyasa

Kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Kwamred Nasir Idris ya gargadi malaman addinin Musulunci kan shiga sabgar siyasa.

Gwamna ya yi wannan gargadi ne yayin da aka kammala tafsirin azumin watan Ramadan inda ya ce ya kamata su bar aibata shugabanni.

Idris ya shawarce su da su mayar da mimbari wurin gyara al'umma ba wai kafa ta biyan buƙatar kansu a siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel