Za a Ja Daga Tsakanin Wike da Atiku Kan Shugabancin Jam'iyyar PDP
- Shugabancin jam'iyyar PDP zai iya sake kawo rikici a tsakanin Atiku Abubakar da ministan Abuja, Nyesom Wike
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yana goyon bayan Gabriel Suswam ya zama shugaban PDP yayin da Wike ke goyon bayan Umar Damagum
- Wike da Atiku sun daɗe suna takun saƙa tun bayan zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na PDP shekarar da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dangantaka na ƙara tsami tsakanin Atiku Abubakar da ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan shugabancin jam'iyyar PDP.
Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke shirin gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa karo na 98 a ranar, 18 ga watan Afirilun 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.
Daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a taron har da batun sauke Umar Damagum daga shugabancin jam'iyyar ko ya ci gaba da riƙe muƙaminsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kujerar Damagum na tangal-tangal a PDP
Akwai waɗanda suke ta yin kiraye-kirayen a sauke Umar Damagum domin a zaɓi sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Damagum, wanda tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ne (yankin Arewa) ya zama muƙaddashin shugaban PDP ne bayan kotu ta dakatar da Iyorchia Ayu a watan Maris na shekarar da ta wuce.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Benuwai, Gabriel Suswam da tsohon mataimakin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Emmanuel Agbo na neman kujerar shugabancin jam'iyyyar PDP.
Su wanene Atiku da Wike yake goyon baya?
Jaridar The Nation ta ce yayin da ɓangaren Atiku ke goyon bayan Suswam, Wike da wasu gwamnonin PDP na son Damagum ya ƙarisa wa'adin mulkin Ayu da ya rage.
Wata majiya mai tushe wanda tana cikin jiga-jigan PDP a yankin Arewa ta Tsakiya ya bayyana cewa Wike da ƴan tawagarsa suna son Damagum ya ci gaba da shugabancin PDP.
A cewar majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ƴan tawagar Wike na son yankin Arewa ta Tsakiya ya samar da mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.
Ana son PDP ta ladabtar da Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa na fara kiraye-kirayen a hukunta Nyesom Wike a PDP saboda yaƙar Atiku Abubakar a zaɓen 2023.
Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun rubutawa majalisar gudanarwa ta NWC takarda cewa a dauki mataki a kan irinsu Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng