Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sunayen Jihohi 2 da Za Ta Ɗora Sababbin Gwamnoni a 2024
- Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za ta lashe zaɓen gwamnonin da za a yi a jihohin Ondo da Edo a 2024
- Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya ce idan Allah ya so za su fitar da Gwamna Obaseki da ƴan koransa daga gidan gwamnatin Edo
- Ranar 21 ga watan Satumba za a gudanar da zaɓen gwamnan Edo yayin da a jihar Ondo kuma INEC ta shirya zaɓen ranar 16 ga watan Nuwamba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya ce jam’iyyarsa za ta yi nasara a zaben gwamna da za a yi a jihohin Edo da Ondo.
Za a gudanar da zabe a jihohin Edo da Ondo a ranakun 21 ga Satumba da 16 ga Nuwamba, 2024, bi da bi.
Sanata Basiru ya bayyana cewa alamu na zahiri da suka fito a halin yanzu sun nuna cewa jam'iyyar APC ce za ta ci nasarar a zaɓukan gwamnonin guda biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ayyana babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin jam'iyyar da ta mutu murus, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Basiru ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu.
Wane shiri APC ta yi?
A ruwayar jaridar Vanguard, sakataren APC na ƙasa ya ce:
"Ɗan takarar mu na gwamna tsohon mamban PDP ne amma ya shiga jam'iyyar APC kuma a karon farko jam'iyyar ta lashe kujerar sanata da mazaɓar da Tony Anenih ya fito.
"A zaɓen da ya wuce, APC ta lashe kujerun sanata guda biyu yayin da Labour Party ta ci guda ɗaya, wannan alama ce da ke nuna nasara tamu ce a jihar Edo.
“Muna da yakinin cewa da yardar Allah za mu fitar da Godwin Obaseki da ’yan siyasarsa masu shan shayi daga gidan gwamnati a zaben da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba."
Dangane da zaɓen jihar Ondo kuma, Sanata Basiru ya ce dama jihar tana hannun jam'iyya mai mulki kuma ita za ta ɗora daga inda ta tsaya bayan kammala zaɓe.
Wahala ta kusa ƙarewa a Najeriya
A wani rahoton na daban Duk da ana fama da yunwa da hauhawar farashin kayayyaki, Bola Ahmed Tinubu ya roki ƴan Najeriya su haɗa kai kuma kada su karaya.
Shugaban ƙasar ya faɗa wa ƴan Najeriya cewa su kwana da shirin cewa tattalin arziki zai farfaɗo daga nan zuwa watan Disamba, 2024.
Asali: Legit.ng