Kakakin Majalisa Ya Fadi Dalilin Kin Rantsar da 'Yan Majalisar APC a Filato
- Rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Filato ya ɗauki sabon salo yayin da shugaban majalisar ya yi ƙarin haske kan lamarin
- A wata hira da aka yi da shi ranar Juma’a, Gabriel Dewan ya bayyana cewa har yanzu ƴan majalisar da ba a rantsar ba, ba su cika sharuɗɗan da suka kamata ba
- Dewan ya bayyana cewa an rantsar da tara daga cikin ƴan majalisa 16 da ake rikici a kai, inda ya yi nuni da cewa kotu ta sha bamban da yadda ake tafiyar da majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Filato - A ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Gabriel Dewan, ya bayyana dalilin da ya sa ya rantsar da mambobin majalisar tara cikin 16 na jam’iyyar APC.
Idan dai ba a manta ba an mayar da ƴan majalisar APC 16 zuwa majalisar ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta kori mambobin jam’iyyar PDP 16 da ke riƙe da waɗannan kujeru.
A makon da ya gabata ne shugaban majalisar ya rantsar da ƴan majalisa tara sannan ya bar bakwai, lamarin da ya harzuƙa jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka ki rantsar da ƴan majalisar?
Da yake bayani kan matakin da ya ɗauka a shirin 'Siyasa a Yau' na gidan talbijin na Channels, Dewan ya ce har yanzu sauran mambobin bakwai ba su cika sharuɗɗan da suka kamata ba kafin a rantsar da su.
A kalamansa:
"A wani lokaci a watan Nuwamba, an samu sanarwa a kotu cewa kotun ɗaukaka ƙara ta kori mambobina 16. Sanarwa a kotu ya sha bamban da yadda ake tafiyar da majalisa.
"Ban je kotun ba, ji na yi cewa an kori mambobina 16. INEC ba ta ce min komai ba sannan ba a bani takardun hukuncin kotun ba domin na tabbatar da cewa an kori waɗannan mambobin."
"Abin da ya kamata a yi shi ne INEC ta rubuto min takarda tare da sanya takardun hukuncin kotun a matsayina na shugaban majalisa ta umurceni cewa bisa wannan hukuncin, an umurce mu da mu janye satifiket ɗin da aka ba waɗannan ƴan majalisar mu mayar da shi ga waɗannan ƴan majalisar.
"Saboda haka muna umurtarka a matsayin ka na shugaban majalisa ka bayyana waɗannan a matsayin mambobinka, amma ba a yi hakan ba.
'Yan majalisa sun samu muƙamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya nada korarrun ‘yan majalisar dokokin jiha na jam’iyyar PDP a matsayin hadimansa.
Gwamna Muftwang ya naɗa ƴan majalisu 16 waɗanda kotu ta tsige daga majalisar dokokin jihar Filato a matsayin jami'an hulɗa da jama'a a mazaɓunsu.
Asali: Legit.ng