Dan Majalisa ya Shawaraci Takwarorinsa da Suka Koma Jam'iyyar APC a Ribas Su yi Murabus
- Dan Majalisar Wakilai Uche Harris ya shawarci zababbun 'yan majalisar da suka sauya sheka da su sauka daga mukamasu
- 'Yan Majalisa 27 a jihar Ribas da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP ne suka sauya sheka zuwa APC mai mulki
- Ya ce doka ta ce duk wanda ya sauya jam'iyya kasa da shekara guda da zabe dole ne ya yi murabus domin fuskantar sabuwar jam'iyyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Anambra- Ɗan Majalisar jihar Anambra mai Wakiltar Idemili ta Arewa da Kudu, Uche Harris Okonkwo ya shawarci ƴan majalisar dokokin jihar Ribas da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC daga PDP su yi murabus.
Leadership ta ruwaito cewa ƴan majalisa 27 ne suka koma jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Ribas.
Lamarin da Okonkwo ya bayyana a matsayin:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sabon shafin cin fuska da mutuncin dimokuraɗiyyar ƙasar nan da tsarin kundin mulkin ƙasa."
Ya ce dokar kasar nan ta bayyana cewa duk wanda ya sauya jam'iyya ƙasa da shekara guda bayan an zaɓe shi ba zai ci gaba da riƙe muƙaminsa ba.
Ɗan Majalisar ya ce:
"Ƴan majalisar su yi murabus cikin mutunci, su yi ƙoƙarin nuna soyayyarsu ga jam'iyyar APC a matsayin ƴan jam'iyya marasa muƙami."
Gwamnati na katsalandan a siyasa
Uche Harris Okonkwo ya ce yawan katsalandan da gwamnati ke yi cikin tsarin gudanar da ayyuka ba ƙaramar matsala ce ga dimokuraɗiyya ba.
Thisday live ta ruwaito ɗan majalisar na cewa shi ba ɗan APC ko PDP ba ne, saboda haka ba shi da riba ko faɗuwa cikin sauya shekar ƴan majalisar.
Ya ce:
"Mutunci ne ya kamata ya zama kan gaba ba buƙatar ƙashin kai ba. Kuma kamata yayi ƴan siyasa su daina ƙara ta'azzara rashin kishi a siyasa da shugabanci matuƙar suna kishin kasar nan da gaske.
Majalisar Ribas ta Kori masu sauya sheƙa
A shekarar 2023, majalisar dokokin jihar Ribas ta taɓa korar wasu ƴan majalisa 25 saboda sun koma APC daga PDP.
An ruwaito cewa ƴan majalisar na biyayya ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ya raba jiha da gwamnati mai-ci.
Asali: Legit.ng