Bayan Ganduje Ya Yi Martani, Gwamna Abba Ya Fadi Matakin Dauka a Kansa

Bayan Ganduje Ya Yi Martani, Gwamna Abba Ya Fadi Matakin Dauka a Kansa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu, ya aika da saƙo ga magabacinsa Abdullahi Umar Ganduje
  • Gwamna Abba ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya buƙaci Ganduje ya fuskanci shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi masa a kotu
  • Gwamnan ya kuma bada tabbacin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya binciki shekara takwas na mulkin Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sabon martani ga magabacinsa Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Abba Kabir ya yi magana ne ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilun 2024.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya shirya yin fada da gwamnatin Shugaba Tinubu, bayani sun fito

Gwamna Abba ya caccaki Ganduje
Gwamna Abba ya shirya binciken Ganduje Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta binciki Ganduje kan cin hanci da rashawa da ya tafka cikin shekaru takwas na mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya caccaki Ganduje

Gwamnan ya yi nuni da cewa shekaru takwas na mulkin Ganduje ba komai a cikinsu face gazawa da rashin iya gudanar da mulki.

Ya nuna takaicinsa kan yadda Ganduje ya ce gwamnatin jihar a ƙarƙarshin jam'iyyar NNPP ta gaza.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Gwamna Yusuf ya dage kan cewa Ganduje ya shafe shekara takwas kan mulki wanda ba komai a cikinsu face rashin iya biyan buƙatun al’ummar Kano da son zuciya."
"Watanni takwas da muka yi kan mulki a bayyana yake sun zarce shekara takwas da Ganduje ya ɓata wajen rashin iya gudanar da mulki ta ko ina."

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Gwamnan Arewa ya bai wa mahajjata tallafin maƙudan kuɗi bayan an yi ƙarin N1.9m

Wace shawara Abba ya ba Ganduje?

Ya shawarci Ganduje da ya mayar da hankali wajen kare kansa a kotu, maimakon ci gaba da kunyata kansa a kafafen yaɗa labarai, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Gwamnan ya tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na gurfanar da Ganduje da muƙarrabansa don su fuskanci doka kan abubuwan da suka aikata ba daidai ba.

An bankaɗo badaƙalar Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu takardun kotu sun bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya siyar da wani kamfanin auduga ga iyalansa.

Takardun sun zargi Ganduje da siyar da kamfanin da ke Challawa ga kamfanin Lesage wanda mallakin iyalansa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng