Shugaba Tinubu Ya Naɗa Matashi Ɗan Shekara 36 a Babban Muƙami, Ya Faɗi Wasu Kalamai

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Matashi Ɗan Shekara 36 a Babban Muƙami, Ya Faɗi Wasu Kalamai

  • Injiniya Uzoma Nwagba ya zama sabon manajan darakta/shugaban hukumar ba da lamuni ta Najeriya (CREDICORP)
  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da naɗin Nwagba, matashi ɗan shekara 36 ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ce sabon shugaban hukumar yana da kwarewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Injiniya Uzoma Nwagba a matsayin manajan darakta/shugaban hukumar ba da lamuni ta Najeriya.

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa ne ya tabbatar da wannan naɗi na matashi ɗan shekara 36 a wata sanarwa ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

Tinubu da Nwagba.
Nwagba ya zama sabon MD/shugaban hukumar ba da lamuni ta Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dolusegun
Asali: Twitter

A cewar sanarwan, Injiniya Nwagba yana da shaidar kammala karatun digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci daga makarantar Havard Business.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma yana da kwalin karatun digirin farko a jami'ar Havard da ke birnin Washington DC na ƙasar Amurka.

Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa sanarwan naɗin a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Wasu bayanai kan sabon MD

Kafin wannan naɗi, Injiniya Nwagba ya kasance babban jami’in gudanarwa na bankin masana’antu, mai kula da sashin kananan lamuni da sauran harkokin kudi a bankin.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Shugaban ƙasa na fatan sabon MD na wannan hukuma mai muhimmanci zai yi amfani da kwarewarsa a fannin hada-hadar kudi da fasaha, da kuma irin nasarorin da ya samu wajen tafiyar da harkokin kudi a fadin Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

"Ana fatan ya yi amfani da gogewarsa a sabon muƙamin wajen faɗaɗa damar samun lamuni ga kowane nau'i na ƴan Najeriya da kuma inganta rayuwar ƴan ƙasa."

Tinubu ya kammala binciken Emefiele

A wani rahoton na daban shugaban ƙasa ya ayyana ƙarshen aikin kwamitin da ya gudanar da bincike a babban banki CBN karkashin Godwin Emefiele.

Bola Tinubu ya godewa Mista Jim Obazee da ƴan tawagarsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da wannan aiki mai rikitarwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262