Gwamnan APC Ya Bayyana Babban Abin da Yake Tsoro Gabanin Zaɓen da Jam'iyya Ta Shirya
- Duk da ana ganin abin ba zai zo masa da sauƙi ba, gwamnan jihar Ondo ya nuna fatan samun nasara a zaben fitar da ɗan takara
- Yayin da ake tunkarar zaben gwamna a Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce yana da ƙwarin guiwa doke ƴan takara 15
- Aiyedatiwa ya jaddada yaƙininsa gabanin zaɓen fitar da ɗan takara na jam'iyya mai mulki, inda ya ce babu abin da yake tsoro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya yi fatali da duk wata barazanar ƴan takara 15 da ke hanƙoron samun tikitin jam'iyyar APC mai mulki.
Gwamnan ya nuna ba ya jin tsoron ƴan takarar da zai kara da su a zaɓen fitar da gwani na APC wanda za a yi ranar 20 ga watan Afrilu, 2024.
Aiyedatiwa ya yi wannan furucin ne bayan mayar da fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito, Gwamna Aiyedatiwa da sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, sun mayar da fom ɗin takararsu ranar Alhamis.
Dukkansu sun sayi fom sun cike kana sun mayar hedkwata ta ƙasa yayin da suke faɗi-tashin lashe tikitin takarar gwamna a inuwar APC a zaɓe na gaba.
Ƴan takarar da za su kara da Aiyedatiwa
Waɗanda Gwamna Aiyedatiwa zai kara da su a zaɓen fitar da ɗan takara sun haɗa da Sanata Jimoh Ibrahim, Olusola Oke, Farfesa Francis Faduyile da Funmi Waheed-Adekojo.
Sauran sune mataimakin shugaban APC na Kudu maso Yamma, Isaac Kekemeke, Akinfolarin Samuel, Olusoji Ehinlanwo, Okunjimi Odimayo, Adewale Akinterinwa, da Olugbenga Edema.
Sai kuma Janar Ohunyeye Olamide, Morayo Lebi, Garvey Oladiran Iyanjan da kuma Ifeoluwa Oyedele.
Akwai wanda gwamnan yake tsoro?
Amma Gwamnan ya ce har yanzun babu wanda zai iya doke shi a zaɓe, inda ya ƙara da cewa ba ya tsoron ko daya daga cikin abokan karawarsa, Punch ta rahoto.
"Ina sane da cewa muna da wasu ’yan takara 15 da ke neman wannan ofis, sun cancanta kuma suna da kwarewa, ina girmama su.
"Amma mun san kanmu, mun san su waye su da abin da za su iya aikatawa, mutane ne masu kishin ƙasa, amma ina tabbatar maku babu wani abin tsoro."
- Lucky Aiyedatiwa.
NAHCON ta gargaɗi maniyyata
A wani rahoton kuma Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara gargaɗin mahajjatan Najeriya da su yi hattara da wasu ƴan damfara da suka ɓullo.
Hukumar ta roƙi maniyyata su kai rahoton duk mutumin da ya nemi su ƙara biyan wasu ƙarin kuɗi bayan kuɗin da aka ƙayyade a hukumance.
Asali: Legit.ng