"Nasara Ta Mu Ce" Gwamnan PDP Ya Cire Tsoro, Ya Ce ba Wanda Ya Isa Ya Tsige Shi Daga Kan Mulki
- Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya tsige shi daga mulki har sai wa'adinsa ya kare
- A cewar gwamnan, mutane sun kaɗa masa kuri'unsu a zaɓen 2023 saboda ya cancanti ya kammala wa'adinsa ba tare da tsaiko ba
- Fubara ya rarrashi mutanen jihar Ribas da cewa kar su damu, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya tabbatarwa al'umma cewa babu abin da zai rage masa wa'adi a kan madafun iko.
Fubara ya bayyana cewa mutane sun zabi gwamnatinsa a ranar zaɓe don haka sai ta kammala wa'adin shekaru huɗu kamar yadda doka ta tanada.
Kamar yadda This Day ta ruwaito, Gwammna Fubara ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kowa a jihar Ribas ya tabbatar da cewa mu muka lashe zaɓe kuma mune muka cancanta mu kammala zangon mulkin mi.
"Babu wani abu da zai rage mana wa'adin da kuka bai wa wannan gwamnatin, sai mun kammala."
Fubara ya yi alƙawarin samae da zaman lafiya
Gwamnan ya faɗawa al'ummar jihar cewa ka da su damu kuma su sanya a ransu cewa gwamnatinsa za ta kare rayuka da dukiyoyinsu.
Fubara ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga mambobin ƙungiyar magoya baya (FSB) lokacin da suka kai masa ziyarar nuna ana tare a gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Laraba.
Yayin wannan ziyara, ƙungiyar ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Fubara, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Fubara, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Ribas, Dokta George Nwaeke, ya ce gwamnatinsa ta matasa, mata, maza da duk wani ɗan Najeriya mai kishin kasa da ke yiwa jihar fatan alheri ce.
Fubara ya naɗa tsohon tsagera
A wani rahoton kuma Gwamna Simo Fubara ya ɗaga darajar tsohon shugaban tsageru zuwa matakin Sarki mai daraja ta farko a jihar Ribas.
Siminalayi Fubara ya mika takardar shaida da sandar mulki ga Amanyanabo na masarautar Okochiri, Sarki Ateke Michael Tom.
Asali: Legit.ng