Ganduje Ya Shiga Matsala Bayan Ya Fadi Jihar da APC Za Ta Kwace a 2025
- Jam’iyyar APGA ta caccaki shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje kan shirinsa na ƙwace jihar Anambra daga jam’iyyar
- Sakataren yaɗa labaran APGA na ƙasa, Mazi Ejimofor Opara ya ce ko shakka babu Anambra ta APGA ce
- Opara ya ce ba a labarin APC a Anambra kuma jihar za ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin jam'iyyar APGA
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Awka, jihar Anambra - Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta ce ko shakka babu jihar Anambra da yankin Kudu maso Gabas na jam’iyyar ne.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APGA na ƙasa, Mazi Ejimofor Opara ne ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje kan cewa Anambra ba ta samun ci gaban da ake sa rai ba.
Ganduje ya ce Anambra ba ta samun ci gaba sosai saboda ba ta da alaƙa da gwamnatin tsakiya, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane martani APGA ta yi wa Ganduje?
Opara ya ce mazauna Anambra za su so su san dalilin da ya sa jihar Kano ƙarƙashin Ganduje ta yanke shawarar janyewa daga APC ta koma jam'iyyar NNPP.
A kalamansa:
"Na farko ina mamakin irin ci gaban da jihar Kano ta samu a ƙarƙashin jam’iyyar APC ta Ganduje wanda ya haifar da ƙin jinin jam’iyyar a 2023, inda jama’a suka yanke shawarar zaɓen NNPP kuma a shirye suke su sadaukar da rayukansu domin kare ƙuri'unsu."
Opara ya ce babu ɗuriyar jam’iyyar APC a jihar Anambra, domin haka ya kamata ta yi watsi da tunanin ƙwace jihar daga hannun APGA, rahoton jaridar The Lunch ya tabbatar.
A kalamansa:
"Anambra da yankin Kudu maso Gabas na APGA ne. Babu shakka a kan haka, kuma ko a inda yankin ya yanke shawarar bin gwamnatin tsakiya, jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa ba ita ce mafita ba.”
Ya ce Anambra ta kasance ta zo ta farko a wurare da dama na ci gaba a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Charles Soludo.
'Wa'adi 1 kawai zan yi' - Ubah
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya yi alƙawarin yin wa'adi ɗaya kacal idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Anambra.
Ubah wanda ke wakiltar Anambra ta Kudu ya bayyana haka ne bayan nuna sha'awar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a shekarar 2025.
Asali: Legit.ng