Cushen N3.7trn: An Buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Murabus Saboda Abu 1 Tak

Cushen N3.7trn: An Buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Murabus Saboda Abu 1 Tak

  • Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula a Bauchi sun yi tir da matakin majalisar dattawa na dakatar da Sanata Abdul Ningi
  • Sun yi kira ga Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus domin ba da damar bincike kan zargin cushen kuɗi a kasafin kuɗin 2024
  • Sanata Abdul Ningi ya tada yamutsi a majalisar dattawa bayan ya yi ikirarin an cusa N3.7trn babu cikakken bayan a kasafin kuɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gamayyar ƙungiyoyi masu kishin jihar Bauchi sun yi Allah-wadai da matakin dakatarwan da majalisar dattawa ta ɗauka kan Sanata Abdul Ningi.

Sun kuma yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi murabus daga kujerarsa domin ba da damar bincike kan zargin cushe a kasafin kuɗin 2024.

Kara karanta wannan

Okuama: Shugaban majalisar dattawa ya faɗi waɗanda yake tunanin suna da hannu a kisan sojoji 17

Akpabio da Abdul Ningi.
An sake kira ga Akpabio ya yi murabus Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Umar Sa’idu Maigamo, shi ne ya faɗi haka yayin da ya jagoranci tawagar mambobi zuwa wurin taron manema labarai a sakatariyar NUJ a Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana dakatar Ningi a matsayin "tsararren shiri, nuna fushi, ba bisa ka'ida ba kuma wanda ga kaucewa tsarin dimokradiyya" kan dalilai da dama.

Idan baku manta ba Sanata Ningi ya yi zargin cewa an yi cushen N3.7trn a kasafin 2024 kuma babu wani bayani kan aikin da za a yi da kuɗin.

Wannan ikirari dai ya haifar da hargitsi a majalisar wanda ya kai ga dakatar da shi na tsawon watanni uku.

Ƙungiyoyi a Bauchi sun mayar da martani

A rahoton Leadership, da yake jawabi ga ƴan jarida, shugaban gamayyar ƙungiyoyin Bauchi ya ce maimakon majalisa ta saurari Ningi, sai ta ɗauki matakin da ta tsara.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Akwai yiwuwar sanata zai koma kujerarsa amma da sharadi, Akpabio na cikin matsi

Maigamo ya ce:

"Muna kallon wannan mataki na majalisar dattawa a matsayin wani yunƙuri ba wai kawai na ɓoye gaskiya ba, har da hana Sanata gudanar da ayyukansa da haƙƙin da tsarin mulki ya ba shi.”

A cewar Daily Post, ya yabawa Sanata Abdul Ningi “saboda jajircewa, da tsayawa tsayin daka kan kishin kasa ta hanyar fallasa gazawar da ke cikin kasafin kudin."

An bukaci Akpabio ya yi murabus

"Muna bukatar shugaban majalisar dattawa ya gaggauta murabus ya matsa gefe domin ba da damar gudanar da bincike a kan zarge-zargen kamar yadda dokar majalisar ta tanada."
"Ya kamata majalisar dattawa ta janye dakatarwar da ta yi wa Ningi tare da neman gafarar Sanatan da kuma mutanen yankin Bauchi ta Tsakiya ba tare da bata lokaci ba."

- Umar Sa’idu Maigamo.

Yadda aka samu ƙarin kuɗin shiga a 2023

A wani rahoton na daban Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗin shiga daga asusun tattara kuɗaɗen shiga na tarayya FAAC a 2023.

A wani rahoto da hukumar NEITI ta fitar kwanan nan, matakai uku na gwamnatoci sun samu ƙarin 23.56% idan aka kwatanta da 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262