Shugaba Tinubu Ya Gana da Ƴan Takara 2 da Kusoshin APC Kan Muhimmin Batu a Villa, Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya gana da jagororin jam'iyyar APC reshen jihar Edo a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
- Bayanai sun nuna cewa zaman zai maida hankali wajen warware dukkan wani rikicin cikin gida da APC ta shiga bayan zaɓen fitar da gwani a Edo
- Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci zaman tare da wasu manyan ƙusoshin jam'iyya mai-ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Edo a fadar gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.
Taron ya samu halartar ɗan takarar APC a zaben gwamnan Edo mai zuwa, Sanata Monday Okpebholo, da abokin takararsa, Dennis Idahosa.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa ana sa ran za a tattauna kan saɓanin da ya raba kawunan wasu ƴa ƴan jam'iyyar a wannan zama a ƙarƙashin shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da za a tattauna a zaman, wata majiya ta ce ɗaya daga ciki shi ne domin Idahosa, ɗan takarar mataimakin gwamna ya janye ƙarar da ya kai kotu.
Yadda rikici ya dabaibaye APC a Edo
Idan ba ku manta ba Mista Idahosa ya shigar da ƙara gaban kotu, inda ya kalubalanci sahihancin takarar Okpebholo.
Zaɓen fitar da gwanin da APC ta gudanar wanda aka bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya samu nasara ya bar baya da ƙura.
Sai dai a zagayen farko na zaben fidda gwanin, kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC ta ƙasa ya bayyana cewa bai kammala ba, sakamakon wasu kura-kurai da aka samu.
A wani yunƙuri na sasantawa, jam'iyar APC ta zaɓi Idahosa, ɗaya daga cikin ƴan takara a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna, Daily Trust ta ruwaito.
Jiga-jigan APC da aka gani a Villa
Daga cikin waɗanda aka gani a wurin zaman a ofishin shugaban ƙasa har da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran sun haɗa da sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, tsohon sanatan Edo ta Kudu, Matthew Urhoghide, da sauransu.
Ganduje ya ɗinke ɓarakar APC a Edo
A wani rahoton kuma Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dinke wata ɓaraka da ta kunno kai a jami'yyar.
Jam'iyyar ta yanke hukuncin nada Hon. Dennis Idahosa a matsayin mataimakin 'dan takarar gwamnan jihar Edo.
Asali: Legit.ng