Abdul Ningi: Akwai Yiwuwar Sanata Zai Koma Kujerarsa Amma da Sharadi, Akpabio Na Cikin Matsi
- Akwai yiwuwar Sanata Abdul Ningi zai koma kujerarsa bayan dakatar da shi da aka yi a Majalisa Dattawa
- Wata majiya daga Majalisar ta tabbatar da cewa yanzu haka ana sasatawa domin ganin Ningi ya dawo kujerarsa
- Wannan na zuwa ne bayan dakatar da sanatan har na tsawon watanni uku kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar janye matakin dakatarwa kan Sanata Abdul Ningi da aka yi.
Majalisar Dattawa ta dakatar da sanatan ne kan zargin cushe na tiriliyan 3.7 kasafin kudin shekarar 2024.
Menene rahotanni ke cewa kan Ningi?
Wata majiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ta ce an yi zargin cushen ne domin batawa Majalisar suna a idon duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce amma yanzu haka ana kokarin kawo karshen lamarin cikin ruwan sanyi, cewar Leadership.
Sanatan da ya bukaci a boye sunansa ya ce nan ba da jimawa ba za a iya mayar da Ningi kujerarsa amma da sharadin zai ba da hakuri ga Majalisar.
"Zan iya fada muku cewa babu wata matsala a Majalisar, zargin cushe a kasafin kudi yunkuri ne na batawa Majalisar suna."
"Ana ƙoƙarin batawa Majalisar suna saboda Godswill Akpabio wanda kullum kokari ya ke ya ga an samu daidaito tsakanin majalisar da bangaren zartarwa."
- Cewar majiyar
Dalilin dakatar da Sanata Abdul Ningi
Wannan na zuwa ne bayan dakatar da sanatan har na tsawon watanni uku kan zargin cushe da ya yi a kasafin kudin.
Dakatarwar ta jawo kace-nace daga bangarori da dama a kasar inda aka yi kiran a yi gaggawar dawo da shi.
Gwamna Bala ya goyi bayan Sanata Ningi
Kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya nuna damuwa kan yadda aka dauki mataki kan Sanata Abdul Ningi.
Gwamnan ya ce su na goyon bayan sanatan musamman idan har a kan gaskiya ya ke saboda bin tsarin da ya dace
Hakan ya biyo bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa wanda dan asalin jihar Bauchi ne.
Asali: Legit.ng