Shugaba Tinubu Ya ƙwace Kwamishinan Gwamnan PDP da Babban Muƙami, Sahihan Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya ɗauke kwamishinan ayyukan jihar Ribas bayan ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar BCDA
- Dakta George-Kelly Alabo ya yi murabus daga mukamin kwamishinan ayyuka a gwamnatin Fubara saboda naɗin da Tinubu ya masa
- Alabo na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi murabus a ƙarƙashin Fubara lokacin da rigima ta yi zafi tsakanin gwamnan da ministan Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Kwamishinan ayyuka na gwamnatin jihar Ribas, Dakta George-Kelly Alabo, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Dakta Alabo ya yi murabus daga kujerar kwamishinan ayyuka a Gwamnatin Siminalayi Fubara domim ya karɓi muƙamin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.
Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙar murabus da ya aike ga Gwamna Fubara na jam'iyyar PDP ta hannun ofishin sakataren gwamnatin jihar Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kwamishinan ya yi murabus?
A wasiƙar, Dakta Alabo ya yi bayanin cewa ya ajiye muƙaminsa na kwamishina ne domin ya karɓi muƙamin da Tinubu ya ba shi a gwamnatin Najeriya.
Ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya naɗa Alabo a matsayin darakta janar na hukumar raya yankunan da ke bakin iyaka (BCDA).
Alabo na ɗaya daga ciki kwamshinonin da suka yi murabus daga muƙaminsu ƙarƙashin Fubara a lokacin da rikicin siyasa ya yi zafi tsakanin gwamnan da magabacinsa, Nyesom Wike.
Daga bisani gwamnan ya sake maida shi kan kujerarsa ta kwamishinan ayyuka bayan sulhun da aka yi a fadar shugaban ƙasa.
Bugu da ƙari, Alabo ya yi aiki a matsayin kwamishinan ayyuka karƙashin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Wike.
Yadda rikicin siyasa ya addabi jihar Ribas
Watanni shida bayan hawa kan madafun iko, Gwamna Fubara ya raba hanya da uban gidansa a siyasa, Wike, lamarin da ya haddasa yamutsi a fagen siyasar jihar Ribas.
A wannan lokaci ne majalisar dokoki ta fara shirin tsige Fubara daga kujerar gwamna, lamarin da ya kai ga ƙone wani sashen zauren majalisar.
A karshe, Bola Tinubu ya shiga tsakani kuma aka cimma yarjejeniyar sulhu da ɓangarorin biyu yayin da mafi akasarin ƴan majalisar Ribas suka bar PDP zuwa APC.
Tinubu ya ja hankalin gwamnoni kan shugabanci
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su jingine siyasa kana su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin gina ƙasar nan.
Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a wurin buɗe baki 'Iftaar' na azumin Ramadan a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng