Gwamnan Kano Ya Nemi Tinubu Ya Gaggauta Bude Iyakokin Najeriya, Ya Fadi Dalilinsa

Gwamnan Kano Ya Nemi Tinubu Ya Gaggauta Bude Iyakokin Najeriya, Ya Fadi Dalilinsa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta bude iyakokin Najeriya
  • A cewar gwamnan, bude iyakokin kasar ne kawai hanyar da za ta rage radadin da talakawa ke ciki sakamakon tsadar abinci
  • Abba, ya roki Tinubu ya ba da damar a rika shigo da kayan abinci domin karya farashi da wadatuwarsu a kasar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta duba batun sake bude iyakokin Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito Abba Kabir ya yi nuni da cewa sake bude iyakokin kasar domin shigo da kayan abinci daga kasashen waje zai rage radadin da talakawan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Abba Kabir Yusuf, Bola Ahmed Tinubu
Gwamnan jihar Kano na so Tinubu ya bude iyakoki a shigo da abinci. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan roko ne bayan ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi a gidan gwamnati dake Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimmancin bude iyakokin Najeriya - Abba

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya koka kan halin da ake ciki na yunwa a kasar sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce:

“Ina da yakinin cewa shirin shugaban kasa na bayar da tallafin abinci zai dakile illar karancin abinci idan aka aiwatar da shi.
"Babban matakin gaggawa da zai iya samar da abinci da araha ga al’umma shi ne gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasar tare da ba da damar shigo da kayayyaki kyauta."

Sakon Abba ga hukumar kwastam da Tinubu

Rahoton Premium Times ya nuna cewa Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin bude iyakokin kasar musamman a wannan wata na Ramadan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Ya kuma nuna jin dadinsa da shirin hukumar kwastam na fara rabon kayan abinci ga al’ummar Kano a wannan lokaci na kunci da yunwa da mutane da dama ke fama da su.

Bugu da kari, gwamnan ya ba hukumar tabbacin bada goyon bayansa ga ayyukanta musamman wadanda za su samar da ci gaba ga Kano da Najeriya baki daya.

Gwamna Abba zai gana da Tinubu

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya shirya ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a Abuja inda ya shirya kai masa koke kan halin da talakawa suke ciki.

Yayin da ya roki 'yan kasuwa da su daina boye kayan abinci, Abba ya shaidawa masu ruwa da tsaki na jihar cewa zai gaba da Tinubu don nemo mafita kan tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel