Gwamna Abba Ya Yi Muhimmin Gyara a Babbar Kotun Kano da Kotun Shari'ar Musulunci
- Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin alkalai 9 na babbar kotun jihar Kano da alƙalai huɗu na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci
- Gwamna Yusuf ya buƙaci sababbin alƙalan su yi riko da ƙa'idojin shari'a wajen tafiyar da ayyukansu na shari'a
- Ya ce gwamnatinsa ta kama hanyar bai wa ɓangaren shari'a damar cin gashin kansa domin ya amince da dukkan buƙatunsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci sababbin alkalai 9 da ya naɗa a babbar kotun jihar da khadi 4 na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar Musulunci su yi riƙo da ƙa'idojin shari'a.
Gwamna Abba ya yi wannan furucin ne yayin rantsar da sababbin alƙalan bayan shawarin hukumar shari'a ta ƙasa (NJC) da amincewar majalisar dokokin Kano.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Jumu'a, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen alƙalan da gwamnan ya naɗa
Bature ya ce wadanda aka nada a matsayin alkalan babbar kotun sun hada da Fatima Adamu, Musa Ahmad, Hauwa Lawan, Farida Rabi’u Dan Baffa da Musa Dahiru Muhammad.
Sauran sun haɗa da Halima Aliyu Nasir, Aisha Mahmud, Adam Abdullah, da kuma Hanif Sunusi Yusuf.
kakakin gwamnan ya kara da cewa waɗanda aka naɗa a matsayin alkalan kotun ɗaukaka kara ta shari'ar musulunci (Khadi) sun haɗa da Muhammad Adam Kademi da Salisu Muhammad Isah.
Sauran alkalan da gwamnan ya naɗa a kotun musulunci sune, Isah Idris Said da kuma Aliyu Muhammad Kani, rahoton Solabase.
Ɓangaren shari'a zai samu damar cin gashin kanta a Kano
Da yake jawabi bayan kammala bikin rantsuwar, Gwamna Yusuf ya ce ya nada su ne da tabbacin cewa sun cancanta ta kowane fanni wajen rike wadannan mukamai.
Ya ce gwamnatinsa ta amince da mafi yawan bukatun bangaren shari’a duba da kudirinsa na bai wa sashin shari'a damar cin gashin kanta.
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
A wani rahoton na daban kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani kan garkuwa da ƴan gudun hijira, malamai da ɗalibai a jihohin Borno da Kaduna.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin APC ta gaza samar da abu mafi muhimmanci ga ƴan ƙasa.
Asali: Legit.ng