Dan Ganduje Ya Samu Muƙami da Tinubu Ya Dakatar da Shugaban REA a Kan N2bn

Dan Ganduje Ya Samu Muƙami da Tinubu Ya Dakatar da Shugaban REA a Kan N2bn

  • Bola Tinubu ya dakatar da Ahmad Salihijo Ahmad daga matsayin shugaban hukumar REA tare da manyan daractoci kan almundahana
  • Shugaban ƙasar ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan yadda N2.1bn suka sulale kuma ana zargin da hannunsu
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya naɗa sabbin waɗanda zasu maye gurbinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Manajan Darakta/Shugaba na hukumar wutar lantarki ta karkara (REA), Ahmad Salihijo Ahmad.

Bola Tinubu ya dakatar da Ahmed Salihijo tare da wasu daraktoci uku na hukumar har sai baba ta gani.

Shugaba Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar REA.
Bola Tinubu Ya Dakatar da Shugaban Hukumar REA da Wasu Mutum Kan Badakala Hoto: Ahmad Salihijo Ahmad, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis kuma aka wallafa a manhajar X watau Twitter.

Kara karanta wannan

Ban taba ganin irinsa ba, Hadimin Tinubu ya fadi lokacin da Tinubu ke kwanciya duk daren Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jero sauran wadanda dakatarwan ta shafa, Olaniyi Alaba Netufo, daraktan ayyukan kamfanoni; Barka Sajou, daraktan ayyukan fasaha; da Sa’adatu Balgore, daraktar asusun lantarki na karkara (REF).

Tinubu ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan zargin waɗanda aka dakatar da, "hannu a wata almundahana da ta kai sama da Naira biliyan 1.2 a shekaru biyu da suka wuce."

Sanarwan ta ƙara da cewa tuni hukumomin yaƙi da masu cin hanci da rashawa suka kwato wasu daga cikin waɗannan kuɗaɗe da ake zargin sun wawure.

Shugaba Tinubu ya ba ɗan Ganduje muƙami

Shugaban ƙasar ya naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu kuma daga cikinsu ya naɗa ɗan shugaban APC, Abdullahi Ganduje a matsayin darakta a REA.

Umar Abdullahi Umar Ganduje zai karɓi kujerar daraktan ayyukan fasaha na hukumar REA ta ƙasa. Ga dai waɗanda shugaban ƙasar ya naɗa:

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

(1) Abba Abubakar Aliyu - Manajan darakta/CEO

(2) Ayoade Gboyega - Babban darakta, ayyukan kamfanoni

(3) Umar Abdullahi Umar (Ganduje) - Babban darakta, ayyukan fasaha

(4) Doris Uboh - Babban darakta, Asusun Lantarki na Karkara (REF)

(5) Olufemi Akinyelure - Shugaban sashen gudanar da ayyukan lantarki a Najeriya.

NLC da TUC sun gabatar da buƙatunsu kan albashi

A wani rahoton kuma manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun samu sabanin adadin da ya kamata ya zama mafi ƙarancin albashi a Abuja.

Kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa domin nazari kan albashin ma'aikata ya fara sauraron ra'ayoyin jama'a kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262