Zaben 2027: Jam’iyyar APC a Jihar Arewa Ta Yi Wa Shugaba Tinubu Wani Babban Albashir
- Jam'iyyar APC a jihar Benuwai ta ce ta gamsu da salon mulkin shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shetima
- A yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar suka gudanar da wani taro, sun amince Tinubu a ya fito takarar tazarce a zaben 2027
- Jagoran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, Sanata Tilley Gyado ya bayyana cewa Tinubu ya dauko hanyar farfado tattalin arzikin Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Benue - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Benue ta amince Shugaba Bola Tinubu a ya fito takarar tazarce a zaben 2027.
Jam’iyyar ta kuma kada kuri’ar nuna goyon bayan irin salon mulkin shugaban kasar da mataimakinsa, Sanata Kashim Shetima, Tribune Online ta ruwaito.
'Yan APC sun yabi Ganduje, SGF
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Gadunje na daga cikin wadanda suka sha yabo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yarjejeniyar marawa Tinubu baya dai ita ce shawarar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka yanke a wani taro da suka gudanar a Makurdi ranar Lahadi.
"Tinubu zai kai Najeriya tudun mun tsira" - Sanata Gyado
Manyan dattawa da shugabannin jam’iyyar daga shiyyoyi uku da suka hada da ‘yan majalisar tarayya na yanzu da na baya da ‘yan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi da na gundumomi suka halarci taron.
Vanguard ta ruwaito jagoran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, Sanata Tilley Gyado ya bayyana cewa salon shugabancin Bola Tinubu zai kai kasar zuwa tudun mun tsira.
Ya bayyana cewa tuni shugaban kasar ya fara maido da tattalin arzikin kasar kamar yadda ya ce jihar Benuwai ta karbi naira biliyan 44 daga gwamnati.
Kadan daga ayyukan Tinubu a Benue
Ya lissafta kudin da jihar ta samu da suka hada da, tallafin kayayyakin more rayuwa, janye tallafin man fetur, da kuma kudaden shiga na kasa da kasa.
A cewar Gyado:
“Saka wutar lantarki mai amfani da hasken rana a garuruwan jihar da kuma Makurdi da gwamnatin Tinubu ta yi shaida ce ta kudurin samar da makamashin wuta mai dorewa.
“Sauran shirye-shiryen ci gaba da aka tsara ta hanyar fara aikin hanyar Makurdi zuwa Enugu ciki har da gadar sama a Wurukum a Makurdi ya nuna gagarumin ci gaba."
2027: Kungiyar APC ta fara nemawa Tinubu kuri'a
A wani labari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata sabuwar kungiyar jam'iyyar APC mai suna All Progressives Congress Grassroot Movement (CAGRAM) ta sha alwasin samawa Tinubu kuri'u a zaben 2027.
Engr. Salisu Magaji, shugaban kungiyar na kasa ya bayyana cewa shugaban kasa ya cancanci goyon bayan jam'iyyar saboda ayyukan da ya yi a fadin kasar tun bayan hawa mulki.
Asali: Legit.ng