Gwamnan PDP Zai Ba 'Yan Adawa Mukamai Masu Gwabi a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

Gwamnan PDP Zai Ba 'Yan Adawa Mukamai Masu Gwabi a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jijar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya shirya dama wa da ƴan adawa a mulkinsa karo na biyu a jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa zai ɗauko ƴan jam'iyyun adawa na APC da LP domin ba su muƙamai a gwamnatinsa
  • Ya yi nuni da cewa nasarar da ya samo a zaɓen gwamnan jihar ba ta jam'iyyar PDP ba ce kaɗai, sauran ƴan adawa su ma za su samu rabonsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana cewa mambobin sauran jam’iyyun siyasa da suka haɗa da APC da Labour Party (LP) za su shiga cikin jerin sunayen sabbin kwamishinoninsa.

Diri ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis jim kadan bayan tafiyar zaman lafiya ta mako- mako mai nisan kilomita biyar, wacce ta ƙare a rukunin filayen wasanni na Samson Siasia da ke Yenagoa, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Diri zai ba 'yan adawa mukamai
'Yan adawa za su samu mukamai a gwamnatin Diri Hoto: Duoye Diri
Asali: Facebook

Diri tare da mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, an zaɓe su ne a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Nuwamban 2023, kuma an rantsar da su a karo na biyu a ranar 14 ga watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Diri zai ba ƴan adawa muƙamai?

Ya ce zai nemi shawarwari tare da tabbatar da cewa ya zaɓo kwamishinoninsa daga jam’iyyun siyasar jihar domin kafa gwamnatin haɗaka, rahoton Within Nigeria ya tabbatar.

A kalamansa:

“Ina so in tabbatar muku cewa ba za mu ɗau lokaci mai tsawo ba wajen dawo da kwamishinonin mu domin ba za mu halitto wasu mutanen daga sama ba. Mutanen jihar Bayelsa ne dai za su shiga cikin kwamishinonin kuma mun san kanmu.
"Za mu nemi shawarwari daga ko'ina kuma mu yi la'akari da kowane ɓangare na al'umma da duk abubuwan da suka dace. Zaɓen na ranar 11 ga Nuwamba ba na jam’iyyar PDP ba ne ita kaɗai.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: APC, PDP, LP sun yi martani kan zanga-zangar da NLC ke yi a fadin Najeriya

"Zaɓen ya shafi jam'iyyar APC dama jam'iyyar Labour Party. Don haka kada ku yi mamaki idan kun ga wasu sunaye daga irin waɗannan jam’iyyun saboda kowa ya taka rawar gani a zaɓen."

Nasarar Gwamna Diri Na Tangal-Tangal

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC da ɗan takarta a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa sun kammala gabatar da shaidu kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.

Jam'iyyar APC da Timipre Sylva na ƙalubalantar nasarar da Gwamna Duoye Diri na jam'iyyar PDP ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar, 11 ga watan Nuwamban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng