Kano: Duk da Matakin Kotu Abba Zai Dawo da Rusau Bayan Sake Daukar Muhimmin Mataki Kan Haka

Kano: Duk da Matakin Kotu Abba Zai Dawo da Rusau Bayan Sake Daukar Muhimmin Mataki Kan Haka

  • Bayan cece-kuce kan rusau da Gwamnatin Abba Kabir ta yi, gwamnatin ta sake kafa kwamitin don ci gaba da daukar matakai a jihar
  • Kwamitin zai yi binciken gine-gine da ba su da amincewa kafin gina su don daukar matakai masu tsauri kan masu laifi
  • Wannan na zuwa ne bayan rusau da Abba Kabir ya yi a jihar ya jawo cece-kuce da kushe daga bangarorin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin bincike don tabbatar da zakulo gine-gine ba bisa ka'ida ba.

Har ila yau, kwamitin zai bincika gine-gine da ba su da amincewa kafin gina su don daukar mataki a kai.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Abba zai dauki mataki kan gine-gine ba bisa ka'ida ba a Kano
Abba Kabir ya kafa kwamiti don Binciken gine-gine ba bisa ka'ida ba. Hoto: Abba Kabir, Imran Muhdz.
Asali: Facebook

Menene dalilin kafa kwamitin a Kano?

Shugaban hukumar tsara birane da ci gaba, Ibrahim Yakub Adamu shi ya bayyana haka yayin wani taro kan matsalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yakub ya nuna damuwa kan yadda ake sayar da filayen ba tare da neman amincewar gwamnati ba, cewar Leadership.

Ya kuma gargadi masu aikata haka da cewa su guji fushin hukuma saboda za ta dauki mummunan mataki kansu.

Kakakin hukumar, Bahijja Mallam Kabara ta ce wannan mataki na daga cikin himmatuwar Gwamna Abba Kabir don ganin an inganta bangaren tsara Birni.

Gargadin da gwamnan ya yi a Kano

Bahijja ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Talata 27 ga watan Faburairu inda ta ce Abba na son mayar da Kano ta farko a wannan bangaren.

Kwamitin zai samu jagorancin shugabansa Junaid Abdullahi yayin da sauran za su kasance mambobi, Stallion Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Junaid yayin da ya ke bayani ya gargadi masu siyan filayen da su tuntubi shugabannin unguwa kafin aikata haka don gudun fadawa matsala.

Abba zai biya diyyar rusau

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya amince da biyan naira biliyan 3 ga wadanda aikin rusau ya shafa a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan kasuwa sun maka gwamnan a kotu kan rushe musu shaguna da kadarori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel