Yadda Kwankwaso Zai Gina Tafiyar Siyasa Mai Karfi Kamar Buhari, Lauya Mazaunin Kano Ya Magantu
- Wani lauya mazaunin Kano ya bayyana yiwuwar Sanata Rabiu Kwankwaso wurin gina tafiyar siyasa mai karfi a Arewa
- Umar Sa’ad Hassan ya ce tabbas Kwankwaso ya na da matukar tasiri a siyasa kuma ana mutunta shi sai dai bai kai Buhari ba
- Umar ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce tasirin Kwankwaso a siyasa ta na da karfi musamman a jihar Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Wani lauya mazaunin Kano, Umar Sa’ad Hassan ya bayyana Rabiu Kwankwaso a matsayin dan siyasa da ake mutuntawa.
Lauyan ya ce jigon jam’iyyar NNPP ya na da matukar tasiri a siyasar Arewacin Najeriya duk da bai kai tsohon shugaban kasa Buhari ba.
Menene lauyan ke cewa kan Kwankwaso?
Umar ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce tasirin Kwankwaso a siyasa ta na da karfi musamman a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Kwankwaso ya na da matukar tasiri a siyasa musamman a Kano amma zai yi wahala ya yi tasiri fiye da jihar har sai idan ya hadu da manyan jam’iyyu.
“Buhari ya yi haka tun a shekarun 1984 zuwa 1985 a lokacin, zai yi wahala Kwankwaso ya samu haka.”
Lauyan ya bayyana yadda Kwankwaso zai ginu
Yayin da ya ke magana yadda Kwankwaso zai gina kansa kamar Buhari a Arewacin Najeriya, lauyan ya ce Kwankwaso na bukatar hadin kai da manyan ‘yan PDP da APC da aka batawa rai.
Ya ce gina siyasa da irin wadannan zai taimaka masa wurin kara kafa kansa a sauran jihohi.
Ya kara da cewa:
“Ya kamata ya bude idanunsa a wadannan jihohi, ya samu wadanda basajin dadin jam’iyyunsu a APC da PDP don hadaka da su, haka zai saka ya gina tafiyar siyasa mai karfi.”
Kwankwaso ya yi nasara a kotu
Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya samu nasara a kotu bayan korarsa da aka yi a jam’iyyar NNPP.
Kotun ta yi fatali da korar tasa inda ta tabbatar da cewa har yanzu shi dan jam’iyyar ce ta NNPP.
Asali: Legit.ng