Gwamnan PDP da Majalisar Dokokin Jiharsa Sun Shiga Babbar Matsala Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC
- Fararen hula sun gurfanar da Gwamna Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas a gaban babbar kotun tarayya kan sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Enefa Georgewill, ya ce sun nemi kotun ta ayyana kujerun ƴan majalisa 27 a matsayin babu kowa
- A cewarsa ya kamata ƴan majalisun su rasa kujerunsu sakamakon barin jam'iyyar PDP bayan sun samu nasara a inuwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula sun kai ƙarar Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da majalisar dokokin jihar gaban kotu.
Ƙungiyoyin sun kai ƙarar ɓangarori biyu na gwamnati gaban kotu ne kan sauya sheƙar ƴan majalisar jiha 27 daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban ƙungiyar Rivers Civil Society Organisation, Enefa Georgewill, shi ne ya bayyana haka ga wakilin Channels tv ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ƙungiyoyin fararen hular sun bukaci babbar kotun tarayya ta musu fashin baƙi kan sashe na 109 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
A cewarsa, sun nemi karin bayani kan sashin ne domin fahimtar ko ya dace ƴan majalisar su ci gaba da zama a muƙamansu duk da sun bar jam'iyyar da ta ɗauki nauyinsu.
Georgewill ya ɗiga ayar tambaya a yunƙurin ƴan majalisar na sauya wasu dokokin jihar bayan su da kansu suka kafa su domin taimaka wa tsohon gwamna, Nyesom Wike.
Meyasa aka kai Gwamna Fubara ƙara kotu?
A kalamansa ya ce:
"Kungiyoyin farar hula a jihar Ribas guda 6 sun kai ƙarar majalisar dokokin jihar, Gwamna Fubara da wasu jam’iyyu gaban kuliya, inda suka bukaci kotun ta ayyana kujerun ‘yan majalisar 27 a matsayin ba kowa.
"Muna fadin haka ne saboda kujerunsu sun zama babu kowa bayan sun bar jam’iyyar da ta dauki nauyinsu har suka samu nasarar zuwa majalisa, suka koma wata jam’iyya.
"Mun garzayo nan muna rokon kotu ta mana fashin baƙi kan sashe na 109 da ke cewa idan ka sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa, ka rasa kujerar ka."
TUC ya gano mafita a Najeriya
A wani rahoton kuma Ƙungiyar kwadago TUC ta ƙasa ta bayyana abinda take ganin shi ne mafita a Najeriya yayin da ake fama da tsadar kayan abinci.
Yayin hira da ƴan jarida, shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya bukaci Bola Tinubu ya bada damar shigo da abinci daga ƙasashen waje
Asali: Legit.ng