"Ba Wanda Zai So Zama Gwamna Na Shekara 1 Kaɗai" Gwamnan APC Ya Shiga Neman Takara a 2024
- Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bayyana burinsa na tsayawa takara a zaben gwamnan jihar da ke tafe a watan Nuwamba, 2024
- Aiyedatiwa ya ce babu wanda zai so zama gwamnan shekara ɗaya kacal, yana mai cewa kundin tsarin mulki ya ba shi damar ƙara zango ɗaya
- Ya kuma kore duk wani batu da ke nuna ya samu saɓani da tsohon Gwamna Akeredolu kafin Allah ya masa rasuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Lucky Aiyedatiwa, gwamnan Ondo, ya ce zai tsaya takarar gwamnan jihar a zaɓen gwamnan da za a yi a watan Nuwamba 2024.
Gwamna Aiyedatiwa ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takara a wata hira da ya yi da TVC News ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu, 2024.
Ya ƙara da cewa babu wanda zai so ya zama gwamna na shekara ɗaya kacal, don haka zai nemi tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben fidda gwanin da za a yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aiyedatiwa ya ce zai so ya tsaya takara ya kuma lashe zabe mai zuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada na ba shi damar kara wa'adi daya.
Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar gwamna, Aiyedatiwa ya ce:
"Tabbas zan tsaya takara domin na riga na zama gwamna mai ci kuma bari na fada muku wani abu, ba wanda ke son zama gwamna na shekara daya.
"A bani damar da kundin tsarin mulki ya tanada, aƙalla na sake tsayawa takara na zangon ɗaya."
Shin Aiyedatiwa ya samu matsala da tsohon gwamna?
Gwamnan ya kuma musanta cewa ya samu saɓani da tsohon gwamnan jihar, marigayi Rotimi Akeredolu kafin ya rasu.
Aiyedatiwa ya kara da cewa “wasu mutane kalilan ne suka haddasa rikicin siyasa a Ondo a shekarar da ta gabata saboda son ransu."
"Bari na fayyace muku wannan lamarin, babu wani lokaci da wani abu ya haɗa ni faɗa da tsohon mai gidana, bamu taɓa samun saɓani ba, ba rikici a tsakanin mu balle na nemi sasanci.
Peter Obi na shirin sauya sheƙa daga LP?
A wani rahoton na daban Peter Obi ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin tattara kayansa ya fice daga Labour Party (LP) saboda rikicin da ya dabaibayeta.
Tawagar midiya ta tsohon gwamnan 'Peter Obi Media Reach (POMR)' ta ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma wasu bara gurbi ne suka kirkire shi.
Asali: Legit.ng