Ruguntsumin Siyasa Yayin da Kakakin Majalisar Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Ta Baya Kan Kujerarsa
- An samu hayaniya a Majalisar jihar Jigawa yayin da mambobin Majalisar suka yi yunkurin tsige kakakinta, Haruna Aliyu Dangyatin
- Mambobin sun fara shirin tsigewarce yayin da kakakin ke Saudiyya tare da Gwamna Namadi don neman masu zuba hannun jari
- Mambobin na zarginsa da babakere da rashin gudanar da shugabanci yadda ya dace da kuma rashin bin ka’idar aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa – Kakakin Majalisar jihar Jigawa, Haruna Aliyu Dangyatin ya sha da kyar yayin da aka yi kokarin tsige shi daga kujerar.
Mambobin Majalisar daga bisani sun yabawa tsarin shugabancinsa da na Gwamna Umar Namadi.
Mene dalilin shirin tsigewar?
Daily Trust ta tattaro cewa wasu daga cikin mambobin Majalisar ba su jin dadin tsarin mulki na kakakin Majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su na zarginsa da babakere da rashin gudanar da shugabanci yadda ya dace da kuma rashin bin ka’idar aiki.
Hakan dole ta saka kawo jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da NSCDC a harabar Majalisar don tabbatar da tsaro.
Fusatattun mambobin Majalisar sun fara shirin tsige shi ne bayan kakakin Majalisar ya tafi Saudiyya tare da Gwamna Namadi.
Jami’an tsaro da ke harabar Majalisar sun hana shiga da fita cikin Majalisar tare da hana har ma’aikatan wurin shiga cikinta.
Martanin Dangyatin bayan barzanar
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Lawal Shiisu ya ce sun samu bayanan sirri cewa ana son kawo rudani da zai dagula zaman lafiya ne.
Bayan an dawo zaman Majalisar a jiya Laraba 21 ga watan Faburairu, mambobin sun bai wa kakakin Majalisar kuri’ar amincewa da Gwamna Namadi, cewar Tribune.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamna Namadi ne ya shiga tsakani inda ya bukaci mambobin sun janye kudirin da suke shirin yi.
A martaninsa, Dangyatin ya godewa mambobin Majalisar kan irin wannan kara inda ya yi musu alkawarin daidaita komai a shugabancin Majalisar.
Majalisa ta ki amincewa da cire tallafi
Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta ki amince da shirin karin kudin wutar lantarki a kasar inda ake son cire tallafin wutar.
Majalisar ta ce bai kamata a kara kudin yanzu ba ganin irin halin kunci da jama’a ke ciki da kuma mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng