EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Arewa Tsawon Kwanaki 2 Kan Wawushe N10bn, Ta Ɗauki Mataki 1
- Jami'an hukumar EFCC sun ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed a ofishin da ke Ilorin
- Bayanai sun nuna cewa hukumar ta gayyaci Ahamed domin ya amsa tambayoyi kan zargin karkatar da wasu kudi N10bn a lokacin mulkinsa
- Sai dai tunda ya amsa gayyatar ranar Litinin yake tsare kuma alamu sun nuna daga nan sai gaban babbar kotun tarayya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed a ofishinta da ke Ilorin.
Ahmed, wanda ya riƙe kujerar gwamna daga 2011 zuwa 2019, ya shiga komar EFCC ne bisa zargin sama da faɗi da kuɗin baitul-mali da suka kai N10bn.
Har yanzun yana tsare kuma yana fatan samun beli daga hannun EFCC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alamu masu karfi a daren jiya sun nuna cewa EFCC na shirin tasa ƙeyar tsohon gwamnan daga wurin da yake tsare zuwa gaban babbar kotun tarayya da ke Ilorin.
Wane mataki EFCC ke shirin ɗauka kan Ahmed?
Bayanai sun nuna cewa tawagar lauyoyin hukumar EFCC sun dira babban birnin jihar Kwara domin gurfanar da Abdulfatah Ahmed a gaban ƙuliya.
Wata majiya a cikin jami'an hukumar da ta yi magana cikin ƙarfin guiwa ta ce:
"Har yanzu tsohon gwamnan yana tsare a ofishin EFCC domin ci gaba da yi masa tambayoyi. Akwai abubuwa da yawa da zai bada amsoshinsu. Abin dariya ne jin cewa Ahmed ya kai ziyara ne kawai ofishinmu a Ilorin.
Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4
“Zancen gaskiyar shi ne yana da kes na zargin karkatar da Naira biliyan 10. Da zaran an gurfanar da shi a gaban kotu, al’ummar jihar za su san cikakken bayani kan tuhume-tuhumen da ake masa.
"Har yanzu bamu sake shi ba duk da yana ta faɗi tashin ganin ya samu beli, amma ba zamu yi jinkiri ba duba da sabon tsarin shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede."
Za a bada belin tsohon gwamnan?
Amma wata majiyar ta daban ta bayyana cewa da yiwuwar za a ɗauki tsohon gwamnan daga tsare zuwa kotu domin gurfanar da shi.
A cewarta, tawagar lauyoyi daga Abuja sun isa Ilorin domin jan ragamar shari'ar da za a yi wa Abdulfatah Ahmed a babbar kotun tarayya nan da ƴan kwanaki.
Wannan shi ne karo na uku da jami'an EFCC suka titsiye Ahmed bayan gayyatar da suka masa a watan Disamba, 2020, rahoton Leadership.
Gwamnan PDP zai biya matasa alawus duk wata
A wani rahoton kuma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ɗauki alkawarin bai wa matasa ƴan bautar ƙasa alawus na N10,000 kowane wata.
Ya sanar da haka ne ranar Talata yayin da yake buɗe sansanin horar da matasan da ke Damare a karamar hukumar Girei, jihar Adamawa ranar Talata.
Asali: Legit.ng