Ganduje Ya Yi Babban Kamu, Wasu Manyan Jiga-Jigai da Mataimakin Shugaban Majalisa Sun Koma APC
- Jam'iyyar PDP ta rasa wasu manyan ƙusoshi 2 waɗanda suka sauya sheƙa a hukumance zuwa All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara
- Ƴan siyasar biyu ciki harda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki sun ce sun ɗauki wannan matakin ne saboda ci gaban da aka samu a yankinsu
- Shugaban APC na jihar Kwara, Prince Sunday Fagbemi, tare da sauran shugabanni jam'iyyar ne suka tarbi jiga-jigan biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Wasu manyan jiga-jigan Peoples Democratic Party (PDP) a shiyyar Kwara ta Arewa sun sauya sheka a hukumance zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Honorabul Abubakar Suka Baba.
Sai kuma tsohon shugaban ƙungiyar malaman makaranta ta ƙasa kuma tsohon ɗan takarar kujerar majalisar tarayya a inuwar PDP, Abubakar Musa, wanda aka fi sani da Biology.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan ƴan siyasar biyu sun tabbatar da sauya sheƙa a hukumance a wani biki da aka shirya a garin Kaiama, hedkwatar ƙaramar hukumar Kaiama, Leadership ta ruwaito.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Prince Sunday Fagbemi da sauran jagorori ne suka tarbi ‘yan siyasar biyu zuwa cikin inuwar jam’iyya mai mulki.
Haka nan kuma shugaban ƙungiyar Alliance for Sustainable Kwara (ASK), Malam Razaq Lawal, da ƴan tawagarsa na cikin waɗanda suka yi maraba da jiga-jigan biyu.
Meyasa suka yanke shawarar komawa APC?
A jawabin da suka yi lokuta daban-daban, Baba da Musa sun bayyana cewa manyan ayyukan ci gaban da ake yi a shiyyar Kwara ta Arewa ne suka ja hankalinsu zuwa APC.
Sun ce tun bayan zuwan gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq a 2019, Kwara ta Arewa ta samu ci gaba a gina abubuwan more rayuwa, shiyasa suka ga ya dace su koma jam'iyya mai mulki.
Da yake musu maraba, shugaban APC na jihar, Fagbemi ya tabbatar musu da cewa sun zama ɗaya da kowa, ba za a nuna musu banbanci ba, rahoton Naija News.
PDP ta sake rasa babbaj jigo a Abia
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta rasa tsohon mataimamin kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Ifeanyi Uchendu, wanda ya sauya sheƙa zuwa APC.
Jigon siyasar ya bayyana cewa ya zaɓi shiga APC ne domin yana da burin ɗaga siyasarsa zuwa matakin ƙasa.
Asali: Legit.ng