EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Arewa da Tambayoyi Kan Wasu Biliyoyin Naira, Sahihan Bayanai Sun Fito
- Jami'an hukumar EFCC sun tasa tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tambayoyi kan yadda aka kashe kuɗaɗe a lokacin mulkinsa
- Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara da safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu
- Ahmed ya jagoranci jihar Kwara da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya daga 2011 zuwa 2019, inda ya miƙa mulki ga gwamna mai ci na APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC), ta tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.
Kamar yadda Channels tv ta rahoto, EFCC ta titsiye tsohon gwamnan Kwara da tambayoyi kan yadda aka kashe wasu maƙudan biiyoyin Naira lokacin da yake matsayin gwamna.
An tattaro cewa Abdulfatah Ahmed ya isa ofishin hukumar EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara tun da safiyar yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan kuma a yanzu haka yana can jami'ai sun tasa shi a gaba yana amsa tambayoyi kan yadda aka ɓatar da kuɗaɗe a gwamnatinsa.
Ahmed ya kasance gwamnan jihar Kwara da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya tsakanin watan Mayun 2011 zuwa watan Mayun 2019.
Bayan kammala wa'adin shekaru takwas kamar yadda doka ta tanada, Ahmed ya miƙa mulki ga sabon Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
Wane zargi ake wa tsohon gwamnan Kwara?
A ruwayar The Nation, wata majiya ta ce:
"Tsawon sa'o'i bakwai da suka wuce yana can ana bincikarsa, ya rubuta rahoto. Duk da babu cikakken bayanin kan kes ɗin amma ina tunanin yana da alaƙa da karkatar d N9bn a lokacin mulkinsa.
"Akwai yiwuwar zai amsa tambayoyi kan lokacin da ya rike kwamishinan kuɗi a mulkin Bukola Sataki, tsohon shugaban majalisar dattawa."
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya amsa gayyatar da suka masa. Amma daga nan bai yi ƙarin bayani ba.
Ma'aikata sun sassauta buƙatarsu ga Tinubu
A wani rahoton kuma Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya tsaf domin sassauta bukatar ta na neman Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Wannan na zuwa ne duba da yadda yanayi ya sauya wanda ya kunshi tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma faɗuwar darajar Naira.
Asali: Legit.ng