'Yan Kwadago Sun Jero Sabbin Sharuɗda Ga Gwamnatin Tinubu Kan Tsadar Rayuwa, Bayanai Sun Fito

'Yan Kwadago Sun Jero Sabbin Sharuɗda Ga Gwamnatin Tinubu Kan Tsadar Rayuwa, Bayanai Sun Fito

  • Ƴan kwadago zasu zauna da wakilan gwamnatin tarayya ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024 kan batun tsadar rayuwa da albashi
  • Wannan taro na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago (NLC) ta ƙasa ke shirin tsunduma yajin aiki a ƙarshen watan da muke ciki
  • Legit Hausa ta tattaro cewa bayan a farko sun nemi Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi ƙarancin albashi, ƴan kwadago sun sassauta buƙatarsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya tsaf domin sassauta bukatar ta na neman Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata.

Wannan na zuwa ne duba da yadda yanayi ya sauya wanda ya kunshi tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma faɗuwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi muhimmin abu 1 jim kaɗan bayan ya dawo daga birnin Addis Ababa

Shugaba Tinubu da NLC.
Yan Kwadago Sun Gindaya Sabbin Sharudda Kan Gwamnatin Tinubu, Bayanai Sun Fasu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigerian Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa kwamitin da aka kafa kan mafi ƙarancin albashi zai fara zama yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024 domin fara tattauna albashin ma'aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin dai ya ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, tawagar ƴan kwadago da kuma ɓangaren masu zaman kansu.

Kwamitin, wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar ranar 30 ga watan Janairu, ana tsammanin zai miƙa rahotonsa kafin ƙarshen watan Maris, 2024.

Wane sharuɗɗa NLC ta gindaya wa FG?

Da yake tsokaci gabanin taron, Benson Upah, mai magana da yawun NLC, ya ce dole kwamitin ya zo da mafi ƙarancin albashin da ya yi daidai da halin da ake ciki.

A rahoton The Punch, Upah ya jaddada cewa kwamitin zai ɓullo da sabon albashin da zai magance wahalhalun ma'aikata da ma ƴan Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala ta ɓullo a gidajen man fetur a Abuja yayin da NARTO ta ɗauki mataki 1 rak

Haka nan wani babban ƙusa a NLC da ya buƙaci a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da ƴan jarida, ya ce:

"Duk abinda ƴan kwadago zasu buƙata zai zama a zahirance, mafi ƙarancin albashin zai zo daidai da yanayin rayuwar da ake ciki bisa la'akari da abubuwan da ma'aikata ke fuskanta yau da kullum.
"Adadin nawa mutum ke buƙata wajen ɗaukar dawainiyar iyali daidai gwargwado a Najeriya? Alal misali iyalin da ya haɗa iyaye biyu da yara huɗu. Farashi na ɗaya daga cikin abinda NLC ke dubawa.
"Muna kuma duba zahirin albashi, N30,000 da aka amince a 2019 ya kai yadda ake buƙata a 2024 da muke ciki?"

Wani ma'aikacin FG, Nura Aliya, ya shaida wa Legit Hausa cewa tabbas ma'aikata na buƙatar ƙarin albashi saboda tsananin halin da aka shiga na tsadar kayayyaki.

A cewarsa, ƙaramin ma'aikaci kamarsa a yanzu ba ya iya riƙe iyalansa, ƴan uwa da iyayensa.

Kara karanta wannan

Kamfanin BUA zai yi wa ma'aikatansa abu 1 bayan ya kara farashin buhun siminti

Ya ce:

"Ma'aikata sun shiga wani hali, a yanzu albashi ba ya riƙe mutum a wata domin duk wasu kayayyakin amfani na yau da kullum sun nunka farashi amma shi albashin yana nan yadda yake."

Sai dai ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wani lokacin idan ƙungiyar kwadago ta taso kamar zata yi yaƙi sai kuma ta yi sanyi.

Mutane sun sake fitowa zanga-zanga kan tsadar rayuwa

A wani rahoton kuma Zanga-zanga ta barke a jihar Oyo a ranar Litinin kan tsadar rayuwa, tsadar abinci da kuma tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Zanga-zangar da aka fara ta daga unguwar Mokola da ke Ibadan, babban birnin jihar, an ga matasa rike da kwalaye da ke dauke da rubutuka na nuna bacin rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel