Zaben Edo: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Janye Daga Takara, Ya Fadi Dalilansa

Zaben Edo: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Janye Daga Takara, Ya Fadi Dalilansa

  • Zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC na neman kujerar gwamnan jihar Edo ya fara ɗaukar wani sabon salo
  • Ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴan takarar, Fasto Osagie Ize-Iyamo, ya girgiza mutanen Edo a lokacin da ya bayyana janyewa daga takarar gwamna
  • Ya ce ya yanke shawarar ne bayan ya kammala tuntuɓar dangi da abokansa da abokansa na siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Benin, Edo - Kwana ɗaya gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, fitaccen ɗan takara Fasto Osagie Ize-Iyamu ya bayyana ficewarsa daga takarar gwamna.

Fasto Ize-Iyamu ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aikewa muƙaddashin shugaban jam’iyyar na jihar, Jarrett Tenebe, inda ya bayyana irin wahalar wannan zaɓin nasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ayyana yin azumin kwana 1 a Borno, ya fadi dalili

Ize-Iyamu ya janye daga takara
Ize-Iyamu ya hakura da yin takarar gwamnan jihar Edo Hoto: Pastor Osagie Ize-Iyamo
Asali: Facebook

Malamin addinin ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne bayan ya tuntuɓi iyalansa da abokansa da abokansa na siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani jawabi da Osagie ya yi, ya bayyana cewa:

"Na shiga takarar gwamnan jihar Edo a 2023 ne sakamakon kishi da jajircewa na na ganin an ceto jihar Edo daga halin da take ciki.
"Bayan tattaunawa mai zurfi da ƴan uwa, abokaina, da abokaina na siyasa, mun yanke shawarar cewa zan janye daga takarar gwamna."

Dan majalisa ya musanta samun goyon bayan Oshiomhole

A halin da ake ciki, Dennis Idahosa, ɗan majalisar wakilai da ke neman takarar gwamna a jihar Edo, ya bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan jihar Adam Oshiomhole bai yi masa alkawarin goyon baya ba.

Idahosa ya jaddada cewa Oshiomhole ba shi ne uban gidansa na siyasa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana wanda APC zata baiwa tikitin takarar gwamnan jihar Edo a 2024

Wasu ƴan takara na zargin Oshiomhole na goyon bayan Idahosa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a yau kuma sun ƙuduri aniyar adawa da duk wani yunkuri na ɗora dan takara a jam’iyyar.

Idahosa ya fayyace cewa ziyarar da ya kai wa Oshiomhole domin ya sanar da shi burinsa na siyasa ne kawai, matakin da duk masu son tsayawa takara suka ɗauka.

Ɗan Takarar Gwamnan APC Ya Janye

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamna a jihar Edo, Ehiozuwa Agbonayinma ya janye takararsa saboda mutuwar dansa a kwanakin baya.

Yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Ehiozuwa ya bukace su da su goyi bayan duk wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng