Kano: Fitaccen Dan Kasuwa, Dantata Ya Fadi Tsarin Mulki da Ya Fi Dacewa da Kasar, Ya Fadi Dalili

Kano: Fitaccen Dan Kasuwa, Dantata Ya Fadi Tsarin Mulki da Ya Fi Dacewa da Kasar, Ya Fadi Dalili

  • Yayin da ake kokarin sauya tsarin mulkin Najeriya, shahararren dan kasuwa ya bayyana matsayarsa kan kudirin
  • Fitaccen dan kasar a Kano, Alhaji Aminu Dantata ya ce babu tsarin da ya fi dacewa da kasar illa na Fira Minista
  • Dan kasuwar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 15 ga watan Faburairu a Kano lokacin da wasu ’yan Majalisar Wakilai suka ziyarce shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Shahararren dan kasuwa a Kano, Alhaji Aminu Dantata ya bayyana tsarin da ya fi dace wa da Najeriya a yanzu.

Dantata ya ce tsarin shugabancin Fira Minista da wasu ’yan Majalisar suke nema shi ne mafi alkairi ga kasar a yanzu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya fadi masifar da za ta faru idan ba a dauki mataki ba, akwai dalilai

Dantata ta yi magana kan tsarin mulkin Najeriya
Aminu Dantata Ya Fadi Tsarin Mulki da Ya Fi Dacewa da Najeriya. Hoto: Aminu Dantata.
Asali: Twitter

Dantata ya fadi tsarin da ya fi

Fitaccen dan kasuwar, ya bayyana haka ne a yau Alhamis 15 ga watan Faburairu a Kano lokacin da ’yan Majalisar Wakilai suka ziyarce shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Majalisar karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda sun ziyarci dan kasuwan ne don neman shawara kan kudirin da suke kokarin dabbakawa.

A cewarsa:

“Nagode da ziyara kuma ina yi wa wannan gagarumin gangami addu’ar samun nasara a ayyukanku.
“Tsarin Fira Minista ne ya fi dacewa da Najeriya saboda rage yawan kashe kudade ba kamar tsarin shugaban kasa da muke ciki ba a yanzu."

Sakon Dantata ga mambobin Majalisar

“Ina fatan za ku samu goyon bayan abokan aikinku, kuma ina muku fatan nasara da karin basira, Allah ya yi muku jagora wajen cimma wannan kyakkyawan manufa ta ku.

Kara karanta wannan

An samu hayaniya bayan 'yan Majalisa 60 sun bukaci sauya fasalin mulkin Najeriya, bayanai sun fito

Tun farko, jagoran tawagar, Hon. Kingskey ya tabbatarwa Dantata cewa wadanda suka kawo kudurin za su yi duk mai yiyuwa don tabbatar da kasancewarta.

Ya ce sun kirkiro kudirin ne da zuciya mai kyau bayan yin nazari kan tsarin Fira Minista da alkairin da ke ciki, cewar Tribune.

'Yan Majalisar Wakilai sun bukaci sauya tsarin mulki

Kun ji cewa akalla 'yan Majalisar Wakilai fiye da 60 ne suke neman sauya tsarin mulkin Najeriya.

Mambobin Majalisar sun bukaci sauya tsarin mulkin shugaban kasa da ake yi yanzu zuwa na tsarin Fira Minista.

Tsarin Fira Minista dai shi ne mulkin da aka fara yi tun farkon samun 'yancin kan Najeriya inda aka bai wa Abubakar Tafawa Balewa Fira Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.