An Samu Hayaniya Bayan 'Yan Majalisa 60 Sun Bukaci Sauya Fasalin Mulkin Najeriya, Bayanai Sun Fito

An Samu Hayaniya Bayan 'Yan Majalisa 60 Sun Bukaci Sauya Fasalin Mulkin Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Da alamu mambobin Majalisar Tarayya sun gaji da tsarin mulkin Najeriya inda suka bukaci sauyi a tsarin mulki
  • Akalla mambobin Majalisar 60 ne suka bukaci sauya tsarin da ake yi zuwa tsarin da ke dauke da Fira Minista kamar yadda aka faro a kasar
  • Mamban Majalisar daga jihar Legas, Wale Raji shi ya jagoranci mambobin don neman sauyi a kundin tsarin mulkin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mambobin Majalisar Wakilai akalla 60 ne suka bukaci sauya yadda ake mulki a Najeriya zuwa wani daban.

'Yan Majalisar sun bukaci a yi gyaran fuska tare da sauya tsarin mulki da ake yi zuwa tsarin Majalisa mai dauke da Fira Minista.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Majalisar Wakilai ta nemi sauya tsarin mulkin Najeriya
'Yan Majalisa 60 Sun Bukaci Sauya Fasalin Mulkin Najeriya. Hoto: House of Reps, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene bukatar mambobin kan mulkin Najeriya?

Mamban Majalisar daga jihar Legas, Wale Raji shi ya jagoranci mambobin don neman sauyi a kundin tsarin mulkin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin hujjojinsu akwai rage yawan kashe kudade wurin gudanar da mulki da samar da tsare-tsare, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Har ila yau, masu goyon bayan kudurin sun tabbatar da cewa sabon tsarin ba zai fara aiki yanzu ba, zai iya kai wa zaben shekarar 2031.

Yadda tsarin mulkin da ake bukata ya ke

Kudurin ya na neman a yi gyaran fuska a kundin tsarin mulkin kasar na 1999 har zuwa jihohi da kananan hukumomi.

Tsarin da suke bukata shi ne mai dauke da Fira Minista da kuma shugaban kasa wanda aka fara tun bayan samun 'yancin kai, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Tsarin dai shi ne wanda ke dauke da Fira Minista da kuma shugaban kasa wanda ba shi da wani iko mai karfi a kasar musamman a siyasance.

Tinubu zai shilla kasar waje

Kun ji cewa, shugaban kasa, Bola Tinubu a gobe Alhamis 15 ga watan Faburairu zai tafi kasar Habasha.

Tinubu zai tafi birnin Addis Ababa ne da ke kasar don halartar babban taron kungiyar kasashen Nahiyar Afirka (AU).

Za a gudanar da taron ne a karo na 37 wanda shugabannin kasashen Nahiyar da dama za su halarci taron mai muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel