Ganduje Ya Kara Gurgunta Jam'iyyar PDP Yayim da Manyan Jiga-Jigai da Dubban Mambobi Suka Koma APC

Ganduje Ya Kara Gurgunta Jam'iyyar PDP Yayim da Manyan Jiga-Jigai da Dubban Mambobi Suka Koma APC

  • Jam'iyyar PDP ta sake gamuwa da babban cikas yayin da dubannin mambobi suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Manyan jiga-jigai da mambobin jam'iyyun ZLP da PDP sun canza sheƙa zuwa APC yayin da ake shirin zaben gwamnan jihar Ondo a 2024
  • Shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya faɗa wa masu sauya shekar cewa su ɗauka sun zo gida, ba za a nuna masu banbanci ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kara samun koma baya a jihar Ondo yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a cikin shekarar 2024.

Ƙusoshi da mambobin PDP akalla 2,000 ne suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jam’iyyar PDP ta gaji da adawa marar amfani, za ta taimaki APC kan matsalar

Dubunnai sun koma APC a jihar Ondo.
Zaben Ondo: Jam'iyyar APC ta karbi masu ssuya sheka 2000 daga PDP da ZLP Hoto: PDP, APC
Asali: Twitter

Haka nan kuma wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) sun bi sahu zuwa jam'iyyar APC mai mulkin jihar Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin masu sauya sheƙar harda tsohon ɗan takarar mamban majalisar tarayya, Dare Aliu, Dakta Felder Olatunji Adeoye, Honorabul Prince Olu Falolu da Anodele Ikumawoyi.

Fasto Olatunde Felix, Cif Pius Akinrinmola, Isaac Olaleye, Alhaji Adebayo Oyewumi, Yele Akinya, Cif Akinmoye Ajewole, Adegborioye Sunday da sauransu na cikin masu sauya sheƙar.

Ba zamu nuna muku banbanci da saura ba - Shugaban APC

Da yake karbar wadanda suka sauya sheka, shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya ce sauran jiga-jigan siyasa da suka rage a PDP sun dawo cikin ‘yan uwa masu son ci gaba.

Adetimehin ya bayyana cewa PDP ta zama gawa a jihar, inda ya ce za a yi wa wadanda suka sauya adalci da daidaito a APC.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na jihar Arewa, ta faɗi sahihin mai kujerar

Ya ce:

"Sauran ƙusoshin da suka rage a PDP sun baro ta a jihar Ondo, PDP ta zama gawa. A jihar Ondo APC da gwamnati duk abu ɗaya ne.
"A koda yaushe muna aiki tare sabida haka tun da kun shigo APC, babu wani zancen tsohon mamba da kuma sabo, mun zama ɗaya tun daga matakin gunduma da ƙaramar hukuma."

LP ta dakatar ma'ajiyi ta ƙasa

A wani rahoton na daban Rigimar cikin gida a jam'iyyar LP ta ɗauki sabon sabo yayin da fitacciyar jam'iyyar adawan ta ɗauki tsattsauran mataki kan babbar jigo.

LP ta sauke ma'jiyi ta ƙasa daga kan muƙaminta kan rikicin da ya shiga tsakaninta da shugaban jam'iyya na ƙasa, Julius Abure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262