Jigon PDP Ya Yi Wa Tinubu Wankin Babban Bargo, Ya Gargadi Abba Gida Gida Kan Abu 1 Tak

Jigon PDP Ya Yi Wa Tinubu Wankin Babban Bargo, Ya Gargadi Abba Gida Gida Kan Abu 1 Tak

  • An bayyana Shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin wanda ya dauki siyasa sana'a, inda ya fi mayar da hankali kan siyasa da 2027 fiye da yadda yake tafiyar da mulki
  • Da yake zantawa da jaridar Legit, Rilwan Olanrewaju, jigon jam'iyyar PDP, ya magantu kan kiran da APC ke yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano na barin NNPP
  • Jigon na PDP ya shawarci gwamnan Kano da ya duba bayan 2027 sannan ya gina NNPP ta zama jam'iyyar adawa mai karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya bayyana Shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin mutumin da ya dauki siyasa aiki, wanda ya fi mayar da hankali ga siyasa da zaben 2027 fiye da yadda yake jagoranci.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

A wata hira da jaridar Legit, Olanrewaju ya ce Tinubu ya yi watsi da kawo ci gaba a Najeriya.

Jigon PDP ya gargadi Abba kan komawa APC
Jigon PDP Ya Yi Wa Tinubu Wankin Babban Bargo Ya Gargadi Abba Gida Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jigon na PDP ya yi tsokacin ne yayin da yake martani ga kiran da shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi kan Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya dawo jam'iyyar mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ta rade-radin cewa Gwamna Yusuf, wanda aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar NNPP, yana kan hanyarsa ta komawa APC tun bayan sakamakon hukuncin Kotun Koli da ya dawo da shi kan kujerarsa bayan kotun kasa ta tsige shi.

Dalilin da yasa kasa Abba Yusuf ya koma APC ba

A martaninsa, Olanrewaju ya yi zargin cewa Tinubu ne ya kitsa kiran. Ya shawarci gwamnan Kano da ya dubi bayan 2027 sannan ya gina NNPP ta zama jam'iyyar adawa mai karfi.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a jam'iyyar Labour, ana zargin Julius Abure ya karkatar da naira biliyan 3.5

Ya ce:

"Tinubu ya rigada ya watsar da batun kawo ci gaba a Najeriya. Ya mayar da hankali kan siyasa da 2027, wanda ba abu ne mai kyau ga talakawan Najeriya ba.
"Akodayaushe kuskure ne kawo wanda ya dauki siyasa sana'a a matsayin shugaban kasa saboda babban abin da za a sanya gaba shine siyasa ba mulki ba.
"Ina fatan Gwamna Abba zai iya duba bayan 2027 sannan ya mayar da hankali wajen sanya NNPP ta zama babbar jam'iyyar adawa a fadin kasar."

Talaka ne ya janyo halin da ake ciki, Buba Galadima

A wani labarin, mun ji cewa Buba Galadima ya daura laifin halin da ake ciki a yanzu akan talakan Najeriya.

A wata hira ta musamman da Legit Hausa tayi da Galadima, ya nanata cewa sai da ya yi hasashen yanayin da ake ciki kafin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng