Tsadar Rayuwa: Na Hannun Daman Atiku Ya Soki Masu Zagin Tinubu Kan Halin Kunci, Ya Fadi Dalilai
- Jigon PDP kuma tsohon kakakin dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya ce ya kamata 'yan Najeriya su yi wa Tinubu uzuri
- Daniel Bwala ya ce tsadar rayuwa ba iya Najeriya kadai ba ne, matsalar ta shafi duk duniya baki daya
- Yayin da ya ke kwatanta tsadar rayuwa a Najeriya da Ingila ya ce kwalbar manja ana siyar da ita naira dubu 38 a Ingila
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kare matakin Tinubu.
Daniel Bwala ya ce tsadar abinci duk duniya ce ba iya Najeriya kadai ba ne inda ya ce Tinubu ya na bukatar karin lokaci.
Mene Bwala ke cewa kan Tinubu?
Yayin da ya ke kwatanta tsadar rayuwa a Najeriya da Ingila, Bwala ya ce kwalbar manja ana siyar da ita naira dubu 38 a Ingila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, ya ce askin kai kawai idan za ka yi a Burtaniya sai ka biya naira dubu 45 kwatankwacin kudin Najeriya.
A cewarsa:
"Matsalar tsadar rayuwa ba iya Najeriya ba ne, duk duniya ana fama da haka.
"Karamar kwalbar manja kawai sai ka biya dala 20, dubu 38 kenan a Najeriya yayin da sai ka biya naira dubu 45.
"Labari mai dadi shi ne an yi hasashen a karshen shekarar nan farashin zai sauka, mu yi murna mutane na."
Shawarin da Bwala ya bayar kan tsadar rayuwa
Ya ce Shugaba Tinubu ya na iya kokarinsa wurin gano bakin zaren don kawo karshen matsalar da ya samu.
Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi hakuri inda ya ce Tinubu ya na bakin kokarinsa don dakile matsalar.
Ya kara da cewa:
"Kada wani ya rude ku babu wani shugaban kasa ko dimukradiyya da babu matsaloli, ku bar surutu dan takararka ma zai lalace fiye da haka."
Barau ya yabawa Tinubu kan halin kunci
Kun ji cewa, Mataimakin shugaban majalissar Dattawa a Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya yabawa matakin Tinubu kan matakan da ya ke dauka.
Barau ya ce matakin Tinubu na fitar da tan dubu 102 zai taimaka wurin dakile matsalar tsadar kayan.
Asali: Legit.ng