Kano: Dan Majalisar Tarayya a NNPP Ya Gwangwaje ’Yan Jam'iyyarsa da Abin Alkairi, Ya Fadi Dalili

Kano: Dan Majalisar Tarayya a NNPP Ya Gwangwaje ’Yan Jam'iyyarsa da Abin Alkairi, Ya Fadi Dalili

  • Hon. Bello Shehu da ke wakiltar Fagge a Majalisar Wakilai ya yi abIn a yaba wa magoyan bayan jam'iyyar NNPP
  • Shehu ya ware makudan kudade miliyan biyar ga 'yan mazabarsa da magoya bayan jam'iyyar NNPP 50
  • Ya ce ya yi hakan ne don taimaka musu rike kansu ta hanyar fara harkar kasuwanci da zai taimake su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Fagge a jihar Kano, Hon. Muhammd Bello Shehu ya yi abin alkairi.

Bello ya ware makudan kudade har miliyan biyar ga magoya bayan jam'iyyar NNPP guda 50, cewar Tribune.

Dan Majalisar Tarayya Kano ya gwangwaje magoya bayan jam'iyyar NNPP
Bello Shehu ya ce ya yi hakan ne don saka musu da kokari a zabe. Hoto: Hon. Muhammad Bello Shehu.
Asali: Facebook

Wane mataki dan Majalisar ya dauka?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwankwaso ya yi martani kan matakin Tinubu na fitar da abinci, ya roki jama'a

Dan Majalisar ya ce ya yi hakan ne don taimaka musu rike kansu ta hanyar fara harkar kasuwanci da zai taimake su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu ya kuma ce ya yi don saka musu da irin goyon baya da suka ba shi da jam'iyyar NNPP yayin zaben shekarar 2023.

Bikin an gudanar da shi ne a karamar hukumar Fagge inda ya ce 16 daga cikinsu za su samu dubu 200 kowannensu.

Yayin da ya ce bakwai daga cikinsu za su samu dubu 100 sai kuma mutum 20 za su samu dubu 50 kowannensu.

Ya kara da cewa ba da tallafin da aka kaddamar a mazabun Fagge A da Yanmata Gabas zai ci gaba ko wane wata, cewar Independent.

Dalilin sakawa 'yan jami'yyar

Hon. Bello ya kuma ce ya ware wadannan kudaden ne daga cikin aljihunsa inda ya ce ba kudaden aikin mazabu ba ne.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Ya ce:

"Wannan ba kudaden da ake ba mu na aikin mazabu ba ne, daga cikin albashi ne na ware su don taimakawa wadanda suka nuna mana kauna.
"Sun cancaci haka saboda irin kushe-kushe da suka sha a hannun jam'iyyun adawa, yanzu ga shi sune suke musu dariya."

Kwankwaso ya yabawa Tinubu

Kun ji cewa jigon jam’iyyar APC a Kano, Ilyasu Kwankwaso ya yabawa matakin fitar da abinci da Tinubu ya yi.

Kwankwaso ya ce fitar da tan dubu 102 na kayan abinci zai taimaka wurin dakile tsadar abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.